Bidiyon Yadda Gwamna Zulum Ya Zage Da Kansa Ya Daidaita Cunkoson Jama’a A Wajen Daurin Auren Yar Shettima

Bidiyon Yadda Gwamna Zulum Ya Zage Da Kansa Ya Daidaita Cunkoson Jama’a A Wajen Daurin Auren Yar Shettima

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya yi namijin kokari don ganin abubuwa sun tafi daidai a wajen daurin auren diyar Kashim Shettima
  • Zulum da kansa ya taya jami'an tsaro wajen ganin mutane sun buda domin a samu hanyar wucewa saboda yawan cunkoson jama'a
  • Mutane a shafukan soshiyal midiya sun yada da wannan karamci da saukin kai na gwamnan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - A ranar Asabar 30 ga watan Yuli ne jihar Borno ta yi cikar kwari da mahalarta daurin auren diyar tsohon gwamna kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.

An daura auren ne a fadar Shehun Borno, Mai martaba Alhaji Abubakar Ibn Garbai Umar El Kanemi.

Sai dai an samu cunkoso sosai saboda daurin auren ya yi jama’a sosai kama daga manyan yan siyasa, manyan yan kasuwa masu fada aji da sauransu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Kashim Shettima Yayin da Yake Sanyawa Diyarsa Fatima Albarka , Ya Yi Mata Kyautar Kudi Da Makulin Mota

Zulum
Bidiyon Yadda Gwamna Zulum Ya Zage Da Kansa Ya Daidaita Cunkoson Jama’a A Wajen Daurin Auren Yar Shettima Hoto: northern_hypelady
Asali: Instagram

Hakan ne ya sanya wajen ya tushe har babu wajen saka kafa, don haka gwamnan jihar, Babagana Zulum da kansa ya dunga daidaitawa don rage cunkoso a wajen daurin auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani bidiyo da ya yadu a Instagram kuma shafin northern_hypelady ya dora, an gano Zulum da wani jami’in tsaro suna ta kokarin ganin mutane sun buda don a samu hanyar wucewa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Jama’a da dama sun jinjinawa gwamnan a kan wannan abu da ya yi yayin da suka yaba da saukin kansa.

jays.couture ta yi martani:

“Ina kaunar wannan mutumin.”

sami_hafsat ta ce:

“Zulum daya tamkar da miliyan.”

value_active ta ce:

“Gwamnan mu ❤️”

h.h_glowing_secret ta yi martani:

“ Ina kaunar mutumin nan.”

Bidiyon Kashim Shettima Yayin da Yake Sanyawa Diyarsa Fatima Albarka , Ya Yi Mata Kyautar Kudi Da Makulin Mota

Kara karanta wannan

Sokoto: An Gano Gawarwakin Mutum 26 Da Suka Nutse A Ruwa Sakamakon Gumurzu Da Yan Bindiga Da Jami'an Tsaro Suka Yi

A gefe guda, mutanen Kabilar Kanuri na al’adu masu ban sha’awa da ya bambanta su da sauran kabilu da ke yankin arewacin kasar yayin da suke aurar da daya daga cikinsu.

Hakan ce ta kasance a bikin diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takararmataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima.

A ranar Asabar, 30 ga watan Yuli ne aka daura auren Fatima Kashim Shettima da angonta Sadiq Ibrahim Bunu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel