Bidiyon Kashim Shettima Yayin da Yake Sanyawa Diyarsa Fatima Albarka , Ya Yi Mata Kyautar Kudi Da Makulin Mota

Bidiyon Kashim Shettima Yayin da Yake Sanyawa Diyarsa Fatima Albarka , Ya Yi Mata Kyautar Kudi Da Makulin Mota

  • Kamar yadda yake bisa al'adar Kanuri, Sanata Kashim Shettima ya bayyana a taron jama'a don sanyawa diyarsa Fatima albarka a aurenta
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, an gano Shettim a tsugune a wani taron mata yayin da ya gabatarwa diyar tasa makulin mota da kudi
  • A ranar Asabar, 30 ga watan Yuli ne alkawarin Allah ya cika tsakanin Fatima Kashim Shettima da angonta Sadiq Ibrahim Bunu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mutanen Kabilar Kanuri na al’adu masu ban sha’awa da ya bambanta su da sauran kabilu da ke yankin arewacin kasar yayin da suke aurar da daya daga cikinsu.

Hakan ce ta kasance a bikin diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takararmataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima.

A ranar Asabar, 30 ga watan Yuli ne aka daura auren Fatima Kashim Shettima da angonta Sadiq Ibrahim Bunu.

Kara karanta wannan

Bidiyo Da Hotunan Budan Kan Yacine Sheriff, An Mika Ta A Hannun Surukarta, Turai Yar’adua

Sai dai an gudanar da wani shagali na al’ada inda uban amarya ya bayyana a tsakiyar taron mata domin sanyawa diyar tasa albarka a wannan sabuwar rayuwa da ta shiga.

Shettima
Bidiyon Kashim Shettima Yayin da Yake Sanyawa Diyarsa Fatima Albarka , Ya Yi Mata Kyautar Kudi Da Makulin Mota Hoto: northern_hypelady
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani bidiyo da shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano Sanata Shettima tsugune yayin da diyar tasa ke daya bangaren sannan wasu mata suka zagayesu.

Sai Shettima ya gabatar da makulin mota da kuma wata takardar kudi ga diyarsa yayin da wajen ya dauki shewa da gudan farin ciki.

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyo Da Hotunan Budan Kan Yacine Sheriff, An Mika Ta A Hannun Surukarta, Turai Yar’adua

A wani labari na daban, mun kawo cewa an gudanar da shagalin biki na karshe wato ‘budan kan amarya’ Yacine Sheriff wacce aka daura aurenta da angonta Shehu Umaru Yar’adua.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyo: Dankareriyar daham din da Fatima Shettima ta saka wurin wushe-wushe ya dauka hankali

Tun a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli ne aka kulla aure tsakanin dan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Shehu Yar’adua da amaryarsa Yacine Muhammad Sheriff amma sai aka ci gaba da shagulgulan biki.

Kamar yadda yake bisa al’adar mutanen yankin arewacin Najeriya a kan rufe taron biki ne da budan wanda dangin ango kan yi bayan an kai amarya gidan mijinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel