Hotuna Da Bidiyon ‘Babur Day’ Na Auren Diyar Tukur Buratai, Amarya Fatima Ta Hadu Matuka

Hotuna Da Bidiyon ‘Babur Day’ Na Auren Diyar Tukur Buratai, Amarya Fatima Ta Hadu Matuka

  • Tsohon shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya, zai aurar da diyar sa Fatima
  • Tuni aka fara shagulgulan bikin auren wanda za a daura a karshen makon nan, inda aka yi liyafar ‘Babur Day’
  • Hadaddun hotuna da bidiyoyin shagalin sun bayyana a shafukan soshiyal midiya

Ana ta shagulgulan biki na yaran manya a Najeriya tun a cikin makon jiya, kuma a wannan karon ma za a sake komawa jihar Borno ne.

A makon jiya ne aka daura auren dan tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua mai suna Shehu wanda ya lula jihar ta Borno wajen zakulo zukekiyar matarsa Yacine Sheriff.

Hakazalika a wannan makon akwai daure-dauren aure biyu da za a yi a jihar ta yankin arewa maso gabashin kasar na diyar tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima da kuma diyar tsohon shugaban hafsan Soji, Tukur Buratai.

Tuni dai aka fara shagulgulan bikin Fatima Tukur Buratai wacce za a daura aurenta a gobe.

Fatima Buratai
Hotuna Da Bidiyon ‘Babur Day’ Na Auren Diyar Tukur Buratai, Amarya Fatima Ta Hadu Matuka Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shafin fashionseriesng na Instagram ya fitar da wasu bidiyoyi da hotuna daga ‘Babur Day’ na auren Fatima Buratai.

An gano amaryar sanye cikin shiga ta al’ada na kabilar babur wato farar riga da zanin saki, inda aka sha rawa aka girgije.

Bidiyon Yadda Aka Yi Cinikin Fura Tsakanin Yan Uwan Amarya Da Abokan Ango A Wajen Bikin Fatima Garo

A wani labari na daban, ko shakka babu Mallam Bahaushe na da al'adun masu ban sha'awa idan shagalin aure ya tashi, kama daga Kamu, wankar Amarya da dai sauransu.

Hakazalika a wuraren wannan bukukuwa a kan gudanar da yan wasanni na gargajiya domin kayatar da mahalarta taron musamman ma a tsakanin bangaren ango da amarya.

Hakan ce ta kasance a wajen wani kasaitaccen biki da aka yi na wata amarya mai suna Fatima Tijjani Sule Garo da angonta Mahi Salisu Ladan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel