APC Ta Sha Kaye Yayin Wani Kayataccen Gasa Da Aka Yi Wajen Wani Bikin Aure, Labour Party Ta Haye

APC Ta Sha Kaye Yayin Wani Kayataccen Gasa Da Aka Yi Wajen Wani Bikin Aure, Labour Party Ta Haye

  • Bidiyon wani bikin aure ya yi fice a shafukan soshiyal midiya inda aka gudanar da wani gasa mai kayatarwa a wajen taron
  • A cikin bidiyon, an gano amarya da ango rike da kwalaye da APC da Labour Party rubuce a kansu sannan aka nemi yan biki su yi rawa a bayan wanda suke so
  • Abun mamaki, angon da ke dauke da APC bai samu ko mutum daya da ke goyon bayansa ba domin duk an taru ne a bayan amarya mai Labour Party

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya ta yi kaurin suna wajen hada kayataccen liyafar aure musamman ma idan aka yi dacen haduwa da mai gabatar da shiri wato MC wanda ya san kan aikinsa, harma da kirkiran gasa tsakanin amarya da ango.

Wani MC ya kawo sabon salo a wajen wani bikin aure inda ya gabatar da wani gasa wanda ya birge mutane a shafukan soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Bana karbar canji, manyan kudi nake so: Bidiyon 'dan sanda mai karbar cin hanci babu tsoro

Biki bidiri
APC ta sha kaye yayin wani kayataccen gasa da aka yi wajen wani bikin aure, Labour Party ta haye Hoto: @mc_nomicable
Asali: Instagram

An yi gasar ne tsakanin amarya da ango inda suka rike kwalaye daban-daban rubuce da sunayen jam’iyyun siyasa yayin da wasu mahalarta taron za su yi rawa a bayansu don nuna wanda suke goyon baya.

A cikin haka, sai ya zamana angon na rike da kwalin APC ne yayin da amarya ke rike da na Labour Party.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Nan take sai DJ ya saka kida amma sai dukka jama’ar wajen suka tare a bayan amarya wacce ke rike da kwalin Labour Party.

Angon wanda ke rike da APC bai samu ko mutum daya da ke goyon bayansa ba a wajen kuma wannan gasa ya yiwa wadanda suka halarci bikin dadi sosai.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Gloriaaworinde:

“Wannan MC ya mutu oo.”

Ellapearlgodson:

Kara karanta wannan

Daya Daga Cikin Fasinjojin Jirgin Kasa Da Aka Saki, Barista Hassan Ya Sadu Da Yan Uwansa A Bidiyo

“Lol.”

Vincent_henry20:

“Admin din Pdp ya bar shafin .”

Official_esty_luv_:

“Allah ya albarkaci aurenku har abada, ba za ku taba rabuwa ba.”

Addykem:

“Mun bar masu jam’iyyarsu.”

Cikin fushi, budurwa ta wallafa bidiyon yadda tela ya canza sitayel din da ta zaba

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta fada tarkon telanta wanda ya matukar bata mata rai tare da jefata cikin halin tsaka mai wuya.

Queen Nawal ta shayar da mabiya shafukan soshiyal midiya mamaki bayan ta wallafa wani bidiyo a shafin TikTok inda ta nuna irin sitayel din da ta zaba don ayi mata shi.

A farkon bidiyon, an gano wata matashiya sanye da hadaddun kaya kamar an kera su a jikinta saboda tsabar kyau da haduwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel