Cikin fushi, budurwa ta wallafa bidiyon yadda tela ya canza sitayel din da ta zaba

Cikin fushi, budurwa ta wallafa bidiyon yadda tela ya canza sitayel din da ta zaba

  • Wata budurwa ‘yar kasan Ghana ta je shafin Tiktok don nuna bacin ranta a kan wani tela da ta baiwa dinki
  • Queen Nawal ta wallafa bidiyon wani sitayel da ta zaba amma sai gaba daya telan ya canza shi
  • Mabiya shafukan soshiyal midiya da dama sun yi martani, sun tambayi Nawal game da umurnin da ta baiwa telan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata matashiyar budurwa ta fada tarkon telanta wanda ya matukar bata mata rai tare da jefata cikin halin tsaka mai wuya.

Queen Nawal ta shayar da mabiya shafukan soshiyal midiya mamaki bayan ta wallafa wani bidiyo a shafin TikTok inda ta nuna irin sitayel din da ta zaba don ayi mata shi.

Queen Nawal
Cikin fushi, budurwa ta wallafa bidiyon yadda tela ya canza sitayel din da ta zaba. Hoto daga Queen Nawal
Asali: UGC

A farkon bidiyon, an gano wata matashiya sanye da hadaddun kaya kamar an kera su a jikinta saboda tsabar kyau da haduwa.

Kara karanta wannan

Zafafan Hotunan Ummi Rahab Da Angonta Lilin Baba Suna Shan Soyayya

A bidiyo na biyu kuma, an gano Nawal sanye da kayan da telanta ya dinka mata kuma ko kusa kayan basu yi daidai da wanda ta so ayi mata ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu ta inda sitayel din da ta zaba ya yi kama da wanda aka yi mata kama daga wuyan rigar, hannu da ma shi kansa zanin da aka yi amfani da shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Mabiya shafukan soshiyal midiya sun cika da mamaki a kan wannan sitayil din

Bidiyon dinkin ya jefa mutane cikin halin mamaki kuma ya baiwa wasu dariya.

Kalli wasu daga cikin sharhin a kasa:

fabricstudiobyjay:

“Duk da haka ya yi kyau kuma za a iya sanyawa.”

marvie234:

“Saka takalma masu tsini. Saboda baki saka takalmi mai tsini bane.”

——-edith.of.the.goodlife:

“Ya nuna kamala.”

atuma:

“Ta saka gaba a baya ne.”

Kara karanta wannan

Cin Amana: Ta Bi Shawarar Kawarta Ta Rabu Da Saurayinta Kan Cewa Ya Cika Girman Kai, Yanzu Kawar Na soyayya Da Shi

oluwalofunmilayo:

“Da fatan ba ke kika ce telan ya rufe wasu wuraren a naki ba. Don ban san me telanki ke kokarin rufewa ba fa.”

Zafafan Hotunan Ummi Rahab Da Angonta Lilin Baba Suna Shan Soyayya

A wani labarin, Soyayya na kara karfi yayin da zama ke kara dadi tsakanin amarya kuma jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ummi Rahab da angonta kuma mawaki Shua’abu Lilin Baba.

Jarumar ta saki wasu zafafan hotunansu tare da mijin nata suna shan soyayya a shafinta na Instagram.

Sannan ta jaddada irin soyayyar da take yiwa mijin nata, tana mai alfahari da mallakarsa a matsayin abokin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel