Bidiyo: Buhari ka ci amanarmu, ko zuciyar Fir'auna gareka sai haka, Malam Bello Yabo

Bidiyo: Buhari ka ci amanarmu, ko zuciyar Fir'auna gareka sai haka, Malam Bello Yabo

  • Sheikh Bello Yabo, fitaccen malamin addinin Islama dake Sokoto, ya caccaki shugaba Buhari kan halin ko in kula da ya nunawa fasinjojin jirgin kasa dake hannun 'yan ta'adda
  • Malam Yabo yace Buhari ya ci amanar 'yan Najeriya kuma ya nuna rashin tausayinsa a fili saboda yana da damar ceto jama'a amma ya nuna rashin adalci
  • Ya tunatar da shugaban kasan yadda yayi ranstuwa da Qur'ani amma yana nuna rashin tausayi kamar Fir'auna, zai bayyana a gaban Ubangji inda bashi da ta cewa

Fitaccen malamin nan na jihar Sokoto, Malam Bello Yabo, ya fito a sabon bidiyo yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari tatas kan yadda yayi watsi da lamarin fasinjojin jirgin kasa da ke hannun 'yan ta'adda.

A bidiyon da malamin ya saki a shafinsa na Facebook, ya sanar da cewa Buhari ya ci amanar 'yan Najeriya kuma Allah zai tuhumesa saboda rantsuwa da yayi da Qur'ani kan cewa zai yi adalci.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mu muka tallata Buhari, dole mu fito mu fadi gaskiya, Naburaska ya cashe gwamnati

Malam Bello Yabo
Bidiyo: Buhari ka ci amanarmu, ko zuciyar Fir'auna gareka sai haka, Malam Bello Yabo. Hoto daga Malam Muhammad Bello Yabo
Asali: UGC

Malamin ya kara da tambayar shugaban kasan idan da matarsa ko 'ya'yansa ne ke hannun 'yan ta'adda, haka zai nuna halin ko in kula?

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalaman malamin:

"Muhammadu Buhari ka ji tsoron Allah, wannan bushewar zuciyar taka tayi yawa, wannan rashin tausayin naka ko kai ne Fir'auna iyakar abinda zaka iya kenan.
"Wannan bushewar zuciya taka tayi yawa, Buhari ka ci amanarmu, ka san irin wahalar da muka yi a kanka, ashe ka san busasshiyar zuciya gare ka, ka san baka da imani, baka da tausayi. Duk mai imani ba zai bar mutane cikin wannan taskun ba.
"Tunda ba 'ya'yanka bane, ga mata, wasu da goyo da kananan yara cikin wannan tasku, cikin wannan bala'i kuma gwamnati ta saka musu ido? Wacce irin gwamnati ce wannan? Wadannan irin mutane ne ku jami'an gwamnati? Ya kamata ku ji tsoron Allah, zukatanku sun bushe da yawa."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Ya kara da tambayar:

"To wai yaya zaku iya fuskantar Ubangiji da hakkin bayinsa da kuka yi banza da shi? Rantsuwa fa kuka yi. Kai Buhari kana Musulmi aka baka Qur'ani kayi rantsuwar zaka yi adalci. Yanzu wadannan ka yi musu adalci?
"A kama su, kana da yadda zaka iya kwato su amma ka kyale su? Don haka ku ji tsoron Allah, ku tausayawa wadannan bayin Allah. Yanzu ya za ku ji da a ce matanku ne da 'ya'yanku da 'yan uwanku aka kama?
"Buhari da a ce matar ka ce cikin halin da matan nan ke ciki ya zaka ji? Toh duk yadda za ka ji haka 'yan uwan wadannan bayin Allah suke ji. Don haka ya kamata ku tausaya musu. Ku ji tsoron Allah, ku sani ba nan za a dawwama ba."

Mansurah ga Tinubu: Zan yi maka kamfen da jinina, kyauta, in ka ceto fasinjojin jirgin kasan Abj-Kd

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Kan Bidiyon Barazanar Sace Buhari Da Yan Ta'adda Suka Fitar

A wani labari na daban, bayyanar bidiyon fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane ya tada hankulan 'yan Najeriya.

A sabon bidiyon da suka saki, an ga yadda suke zane jama'ar da ke hannunsu da sanyin safiya inda fasinjojin ke ta kuka cike da ban tausayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel