2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta

2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta

  • Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) ta shirya wani taro a Abeokuta, jihar Ogun
  • An gayyaci Mai martaba Muhammad Sanusi II a cikin wadanda suka yi jawabi ta yanar gizo
  • Muhammad Sanusi II ya yi tir da yadda ake saba dokar zabe ta hanyar sayen kuri’un mutane

Ogun - Sarkin Kano na 14, Malam Muhammad Sanusi II ya bayyana sayen kuri’u a matsayin wani sharri da ya zama barazana ga tsarin siyasar kasar nan.

Daily Trust ta ce Mai martaba, Muhammad Sanusi II ya yi jawabi ne a wajen wani taro na musamman da cibiyar dakin karatun Olusegun Obasanjo ta shirya.

Muhammad Sanusi II ya na ganin sayen kuri’a yana kawo babban cikas wajen zaben shugabanni.

Taron da aka gudanar ta yanar gizo ya tattauna ne a kan abin da ya shafi kafofin sada zumunta na zamani da kuma sha’anin rashin tsaro da zabe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Biyan Kudin Fansa ya Jawo aka Lakadawa Fasinjojin Jirgin Kaduna-Abuja Mugun Duka

A jawabin na sa, Sanusi II yake cewa sayen kuri’u da aka fito da shi a lokacin kada kuri’a, raina dokar zabe ne, sannan rashin sanin darajar akwatin zabe ne.

Mutane na saida 'yancinsu

Khalifan na Darikar Tijjaniya a Najeriya ya nuna takaicinsa a game da yadda mutane suke nunawa Duniya takardar zabensu bayan sun kada kuri’arsu a sirri.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanusi II
Khalifa Muhammadu Sanusi Hoto: Maikatanga
Asali: Facebook

Wasu mutanen suna yin hakan ne domin ya zama shaida gaban ‘yan siyasa, su gamsar da su cewa sun zabe su domin a biya su kudin kuri’ar da suka bada.

Akwai gyara a dokar zabe

Duk da an inganta dokar zabe, Basaraken yana ganin akwai bukatar al’ummar Najeriya su yi kira ga hukuma da su tabbatar da an yi adalci da kuma gaskiya.

“Daya daga cikin hanyar da ake murde zabe a sabuwar dokar zabe ita ce tsarin sayen kuri’a, kuma wannan rashin bin dokar sirrinta kuri’a ne.”

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

“Dole mutanen Najeriya da al’umma su tashi-tsaye, su tabbatar da sirrin kuri’arsu da tabbatar sirrin zabin da suka yi a lokacin da ake yin zabe.”
“Muna bukatar mu tabbatar da cewa wadanda suka shiga ofis, su ne wadanda muka zaba.”

- Muhammadu Sanusi

Rasuwar Bashir Tofa

A farkon shekara nan ne aka samu rahoto Mai martaba Muhammadu Sanusi ya yi wa jama’ar Kano da Arewa ta’aziyyar rashin Alhaji Bashir Othman Tofa.

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yace mutuwar Dattijon rashi ne ga Najeriya gaba daya, Sanusi II ya ce Marigayin ya nunawa danginsu kauna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel