Iyaye Sun Kwashe Yayansu Daga Makaranta A Abuja Bayan Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Da ke Kusa Da Su

Iyaye Sun Kwashe Yayansu Daga Makaranta A Abuja Bayan Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Da ke Kusa Da Su

  • Biyo bayan hare-haren da ake kaiwa a kasar, daliban Najeriya suna fuskantar kallubale a makarantu bayan yan bindiga sun sake sabon barazana
  • Labarin kai hari a wani gari da ke kusa da babban birnin tarayya da yan bindiga suka kai ya tilasta iyaye kwashe yayansu daga makarantar kwana a Abujan
  • Da farko, yan bindigan sun ce Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne wadanda za su sace nan gaba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - An kwashe dalibai daga makarantar sakandare ta tarayya, FGC, Kwali, Abuja daga dakunan kwanansu bayan harin da yan bindiga suka kai wani gari da ke kusa da makarantar, Daily Trust ta rahoto.

Iyaye sun yi tururuwa zuwa makarantar a ranar Litinin don kwashe yaransu daga makarantar da ke kauyen Sheda, a babban hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ma'aikatar ilimi ta ba da umarnin garkame makarantun gwamnatin tarayya na Abuja

Abuja.
Iyaye Sun Kwashe Yayansu Daga Makaranta A Abuja Bayan Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Da ke Kusa Da Su. Hoto: @daily_trust.
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wakilin Daily Trust, wanda ya ziyarci makarantar a ranar Litinin ya ce ya ga wasu iyaye suna kwashe yaransu.

Abin da wasu mahaifan dalibai suka ce

Mrs Babep Peace, mahaifiyar wani dalibi ta ce ta zo daga Legas ne don kwashe yaranta biyu bayan ta samu kira daga mahukunta makarantar na cewa su taho su kwashe yaransu.

Ta ce an kira ta misalin karfe 4 na yamma, hakan yasa ta biyo motan dare daga Legas zuwa Abuja.

"Misalin karfe 4 na yammacin ranar Lahadi daya cikin yaya na ta kira ni ta hannun masu kula da su cewa makaranta ta ce iyaye su garzayo su kwashe yayansu saboda barazanar harin yan bindiga," in ji ta.

Wana mahaifin dalibi, Mr Obaniyi Oluwatokpe, ya ce yana Kabba, Jihar Kogi, a daren ranar Lahadi shima mahukunta a makarantar suka kira shi.

Kara karanta wannan

Mace Mai Kamar Maza: An Karrama Yar Shekara 59 Da Ke Tuka Motar Haya Don Daukar Dawainiyar ‘Ya’yanta

Ya ce tsoron yan bindigan yasa ya garzayo domin an fada mishi sun yi barazanar kai hari a makarantar.

Wata dalibar makarantar yar aji 2 na babban sakandare, Rebbeca Samuel, wanda aka gani da jakunanta ta shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa yan bindiga sun kai hari a kauyen Sheda a daren ranar Asabar, hakan ya firgita su.

"Misalin karfe 12 na daren Asabar ne lokacin da muke barci kawai muka ji karar harbin bindiga wanda haka yasa makaranta ta ce mu tattara kayan mu mu tafi," in ji ta.

Martanin yan sanda

An aike wa kakakin yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine sakon tes amma bata amsa ba domin jin ba'asi kan batun.

Yan ta'adda sun sha sace dalibai da yawa daga makarantu na sakandare da na gaba da sakandare a sassa daban-daban na Najeriya.

Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Bindige Jami'i Daya Har Lahira a Ondo

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Abuja yayin da aka garkame makarantar sakandare saboda tsoron harin 'yan bindiga

A wani rahoton, yan bindiga sun kashe jami'in dan sanda mai suna Temenu Boluwaji a wani harin da suka kai a caji ofis na Okuta Elerinla a Akure Jihar Ondo.

Yan bindigan sun kai hari caji ofishin a safiyar ranar Litinin, The Cable ta rahoto.

Da ya ke tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar, Odunlami Funmilayo, cikin wata sanarwa ya ce harsashi ta ratsa mamamcin yayin musayar wuta da yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel