Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Bindige Jami'i Daya Har Lahira a Ondo

Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda, Sun Bindige Jami'i Daya Har Lahira a Ondo

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari caji ofis na yan sanda har sun kashe jami'in dan sanda guda daya a Jihar Ondo
  • Odunlami Funmilayo, mai magana da yawun yan sandan jihar Ondo ya tabbatar da harin inda ya ce yan sandan da ke bakin aiki sun dakile harin miyagun ba su shiga ofishin ba
  • Amma Funmilayo ya ce yayin musayar wuta da maharan, sun harbi wani jami'in dan sanda mai suna Temenu Boluwaji kuma ya riga mu gidan gaskiya a hanyar kai shi asibiti

Jihar Ondo - Yan bindiga sun kashe jami'in dan sanda mai suna Temenu Boluwaji a wani harin da suka kai a caji ofis na Okuta Elerinla a Akure Jihar Ondo.

Yan bindigan sun kai hari caji ofishin a safiyar ranar Litinin, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

Taswirar Jihar Ondo.
Yan Bindiga Sun Kutsa Ofishin Yan Sanda, Sun Bindige Jami'i Daya Har Lahira a Ondo. @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar, Odunlami Funmilayo, cikin wata sanarwa ya ce harsashi ta ratsa mamamcin yayin musayar wuta da yan bindigan.

"Yan sandan suna bakin aikinsu kuma sun dakile harin domin bata garin ba su samu ikon shiga caji ofis din ba," in ji Funmilayo.
"Yayin musayar wuta, an harbi daya daga cikin jaruman jami'an mu AP.207538 0INSPR. TEMENU BOLUWAJI, daga baya ya mutu a hanyar kai shi asibiti.
"Kwamishinan yan sanda, CP Oyeyemi Adesoye Oyediran psc, fsi, ya bada umurnin sashin binciken manyan laifuka CIS ta tabbatar an kama wadanda suka kai harin.
"Yana kuma amfani da wannan kafar don karfafawa mutanen jihar gwiwa su cigaba da hallastattun ayyukansu, domin an kusa kawo karshen bata garin."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel