Rashin tsaro: Ma'aikata ta rufe kwalejojin gwamnatin tarayya na Abuja, ana ta kwashe dalibai

Rashin tsaro: Ma'aikata ta rufe kwalejojin gwamnatin tarayya na Abuja, ana ta kwashe dalibai

  • Rahotannin da ke fitowa daga babban birnin tarayya Abuja sun bayyana cewa, an ba da umarnin garkame makarantu a birnin
  • An samu hargitsi yayin da wasu 'yan bindiga suka kai farmaki wani kauye da ke kusa da kwalejin gwamnatin tarayya da ke Kwali
  • Majiyoyi sun bayyana cewa, tuni iyaye suka fara kwashe 'ya'yansu daga makarantu domin gudun abin da zai iya biyo baya na rashin tsaro

FCT, Abuja - Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, saboda fargabar fargabar hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda, ta bayar da umarnin rufe dukkanin kwalejojin gwamnatin tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja, tare da ba da umarnin kwashe dalibai cikin gaggawa.

Jaridar Punch ta tattaro cewa an yanke shawarin ne sakamakon karuwar rashin tsaro da barazana ga rayuka da dukiyoyi da kuma jin dadin daliban da ke birnin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari babban birnin jihar arewa, sun sace shugaban jami'an tsaro da yan mata

An ba da umarnin rufe makarantu a Abuja
Rashin tsaro: Ma'aikata ta rufe kwalejojin gwamnatin tarayya na Abuja, ana ta kwashe dalibai | Hoto: GettyImages/Thomas Imo
Asali: Getty Images

Wasu makarantu suka umurci daliban da su tattara su fice su koma gida nan da ranar Laraba, 27 ga watan Yuli, 2022.

A bangare guda wasu makarantun sun aika sako ga iyaye a ranar Lahadi suna neman kada su tsallake ranar Litinin ba su dauke 'ya'yansu ba, saboda fargaba da fargabar harin 'yan bindiga a birnin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani rahoto da ya yadu a shafukan sada zumunta a ranar Lahadi, wanda ke nuni da cewa an yi harbe-harbe sosai a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kwali, Abuja.

Rahoton dai shi ya sa wasu iyaye garzayawa zuwa makarantar domin tabbatar da lafiyar 'ya'yansu, kana da duba yiwuwar tattara su zuwa gida.

Wasu ma’aikatan Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Bwari su ma sun shaida wa Punch cewa, sun samu umarni daga ma’aikatar ilimi ta tarayya na ba wa dalibai damar barin makarantar kafin ranar Laraba.

Kara karanta wannan

An bayyana sunaye da cikakken bayanan Sojojin fadar shugaban ƙasa da yan ta'adda suka kashe a Abuja

Ma’aikatan sun kuma shaida cewa za a rufe makarantar a yau Litinin ba tare da la’akari da wa’adin na ranar Laraba ba saboda an bukaci iyaye da su zo daukar ‘ya’yansu kafin azahar ranar Litinin.

Me hukumomi suka ce game da hakan?

Kokarin jin ta bakin hukumomi game da lamarin ya ci tura; sai dai wasu iyayen da suka nemi a sakaya sunanayensu sun yi ikirarin cewa sako ya fito daga hukumomin makarantar na sanar da iyaye da su zo su kwashe ‘ya’yansu kafin ranar Litinin da rana.

Punch ta ce bata samu damar zuwa ga Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya Mr. Ben Goong ba, don tsokaci kan halin da ake ciki, kasancewar daraktan bai amsa kiran waya ba ko sakwannin tes.

Sai dai, jaridar People Gazette ta ce ta samu jin ta bakin Ben Goong, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda kamfanin dillacin Najeriya ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaron Villa, sun kashe 8 bayan barazanar sace Buhari

Wakilin Legit.ng Hausa ya tattauna da wani mahaifi; Adamu Ibrahim Muhammad da ke zaune a Zaria kuma yake da da a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Kwali, inda ya shaida yadda ya dauko dansa daga makarantar.

"Dama rashin tsaro yasa na kai shi can daga nan Barewa saboda tsoron me zai iya biyowa baya. Amma na ga Abuja ma ta zama matsala.
"Kafin na karbi sakon makaranta kani na da ke zaune a Abuja ya sanar dani an kai hari gefen makarantar, wannan yasa na ce ya san yadda zai dauko yaron daga makaranta.
"Kashe gari, ya kira wayata yace gashi ya dauko shi, kuma Alhamdulillahi yanzu haka yana tare dashi, kuma na ce ya zo dashi gida nan Zaria a karshen mako."

Tashin hankali yayin da FGC Kwali ta umurci iyaye su kwashe 'ya'yansu saboda tsoron harin 'yan bindiga

A tun farko, Hukumomin Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kwali, Abuja, sun bukaci iyaye da su kwashe 'ya'yansu daga makarantar saboda fargabar harin da ‘yan ta’adda za su kawo.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yan bindiga sun yi wa sojoji kwantan ɓauna, sun buɗe musu wuta a Abuja

Hakan ya haifar da firgici a tsakanin mahukunta da ma'aikata da dalibai da iyayen makarantar, kamar yaddda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Hukumar kula da makarantar ta bukaci iyayen ne da su kwashe ya'yansu sakamakon harin da aka kai a wani kauye da ke kusa, wanda ke da shinge da makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel