Rashin tsaro: Na sa shugabannin tsaro a gaba kan su karar da 'yan bindigan kasar nan, inji Buhari

Rashin tsaro: Na sa shugabannin tsaro a gaba kan su karar da 'yan bindigan kasar nan, inji Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fusata da samun labarin mutuwar dan uwan tsohon shugaban PDP Adamu Mu'azu
  • Shugaba Buhari ya sake jaddadawa 'yan Najeriya cewa, suna ransa, kuma zai kawo karshen matsalar rashin tsaro nan kusa
  • A bangare guda, ya yiwa iyalan Mua'zu ta'aziyya, kana ya bayyana jajensa da addu'ar Allah ya jikan mamacin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya kalubalanci hafsoshin tsaron kasar nan a kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, rahoton Daily Trust.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jajanta wa tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Adamu Muazu kan kisan da ‘yan bindiga suka yi wa dan uwansa da kuma sace ‘yar uwar sa.

Martanin Buhari kan kisan dan uwan shugaban PDP na kasa
Rashin tsaro: Na saka shugabannin tsaro a gaba kan su dawo da zaman lafiya kasar nan, inji Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban kasar, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce lamarin ya sa ya kadu kuma ya fusata shi.

Buhari ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wannan bala’i biyu na musamman mai wucewa ne. Na san yana da matukar wuya a jure nauyin wannan bala'i a cikin dangin ku. Ina jin irin zafin da kuke ji.
“Ina amfani da wannan dama don sake tabbatar muku da sauran ‘yan Najeriya da ke fuskantar barazana a halin yanzu daga ta’asar ‘yan bindiga cewa ba zan bar wata kafa ba wajen ganin an murkushe wadannan makiya na bil’adama a karshe kuma an fatattake su.”

Shugaban ya kara da cewa, ya ba hafsohin tsaro umarnin ragargazar 'yan bindiga, kuma yana da tabbacin za su yi hakan nan ba da jimawa ba, rahoton The Nation.

A kalamansa:

"Tsaro shine abin da ya dame ni a koda yaushe kuma na sa shugabannin hafsoshin tsaro su ci gaba da kokarin ganin sun samar da wata kwakkwarar mafita don kawo karshen wannan barazana."

Ya yi addu’ar Allah ya jikan mamacin ya kuma baiwa iyalansa kwarin guiwar jure wannan bala'i da dura gidansu.

'Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Bas, Sun Kashe Direba, Sun Sace Fasinjoji a Katsina

A wani labarin, a ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan bindiga suka kashe wani direban motar zirga-zirga ta gwamnatin Katsina (KTSTA), Nasiru Yusha’u, bayan da ya yi arba da ‘yan bindiga a kan hanyar Katsina zuwa Jibia.

An ce ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da fasinjojin Yushau bayan sun kashe shi, rahoton gidan talabijin na Channels.

Wani mazaunin kauyen Daddara da ya shaida lamarin da ya faru ya shaida wa gidan talabijin din ta wayar tarho cewa 'yan ta'addan sun far wa motar ne da misalin karfe sha biyu na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel