Hotuna Da Bidiyoyin Ali Modu Sheriff Yana Nasiha Ga Diyar Danuwansa, Yacine da angonta Shehu Yar’adua

Hotuna Da Bidiyoyin Ali Modu Sheriff Yana Nasiha Ga Diyar Danuwansa, Yacine da angonta Shehu Yar’adua

  • Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff ya sanyawa diyar dan uwansa, Yacine Sheriff albarka a aurenta
  • Modu Sheriff ya zaunar da diyar tasa tare da angonta, Shehu Yar'adua, inda ya yi masu nasiha sosai a kan zaman aure
  • A ranar Asabar, 23 ga watan Yuli ne dubban Asabar da suka hada da manyan yan siyasa da masu fada aji a kasar suka shaida daurin aure tsakanin ma'auratan biyu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Borno - A ranar Asabar, 23 ga watan Yuli ne aka kulla aure tsakanin dan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Shehu Yar’adua da amaryarsa Yacine Muhammad Sheriff.

Kamar yadda yake bisa al’ada a kan zaunar da ma’aurata sannan a yi masu nasiha tare da wayar da kansu kan wannan sabuwar rayuwa da za su shiga.

Hakan ce ta kasance a bangaren kawun amarya kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Mosu Sheriff wanda ya zaunar da diyar dan uwan nasa da mijinta Shehu ya kuma hada su ya yi masu nasiha mai ratsa zuciya.

Kara karanta wannan

Hadaddun Hotunan Shehu Yar’Adua Da Amaryarsa Yacine Sheriff Yayin Da Suke Shirin Shiga Daga Ciki

Modu Sheriff yana nasiha
Hotuna Da Bidiyoyin Ali Modu Sheriff Yana Nasiha Ga Diyar Danuwansa, Yacine da angonta Shehu Yar’adua Hoto: keepingupwiththeindimis
Asali: Instagram

A wani bidiyo da shafin weddingpostng ya wallafa a Instagram, an gano amarya Yacine da angon nata durkushe a gaban kawun nata yayin da yake masu fada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An jiyo Modu Sheriff na ce masu a yanzu sun zama daya kuma zaman aure ‘zo mu zauna zo mu saba ne’. ya kuma shafa kan amaryar domin sanya mata albarka wannan sabuwar rayuwa da za ta shiga.

‘Ya Da Uwa Sun Fashe Da Kukan Kewar Rabuwa Da Juna A Wajen Liyafar Bikin Diyar, Bidiyon Ya Taba Zukata

A wani lamari na daban, Wani bidiyo ya bayyana a shafin soshiyal midiya na wata amarya da ta fashe da kuka a wajen liyafar bikinta.

A cikin bidiyon wanda shafin weddingpostng ya wallafa a Instagram, an gano amaryar tsaye rike da hannayen mahaifiyarta a filin rawa inda mai gabatar da shirin ta bukaci da ta fadawa mahaifiyarta tana kaunarta kuma za ta yi kewanta.

Kara karanta wannan

Biki Ake Na Manya: Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu

Da furta kalmar kewa, sai amaryar ta rungume mahaifiyar tata inda suka fashe da kuka su dukka biyun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel