Hadaddun Hotunan Shehu Yar’Adua Da Amaryarsa Yacine Sheriff Yayin Da Suke Shirin Shiga Daga Ciki

Hadaddun Hotunan Shehu Yar’Adua Da Amaryarsa Yacine Sheriff Yayin Da Suke Shirin Shiga Daga Ciki

  • Dan tsohon shugaban kasa, Umaru Musa 'Yar Adua zai angwance a yau Asabar, 23 ga watan Yuli
  • Kyawawan hotunan Shehu Yar’adua da amaryarsa Yacine Sheriff cikin shaukin so da kauna sun bayyana
  • Ko shakka babu da za a samu kyawawan yara a wannan auratayya domin kuwa kyau ne zai hadu da kyau

A yau Asabar, 23 ga watan Yuli ne za a daura auren dan marigayi tsohon shugaban kasan Najeriya Umaru Musa 'Yar' Adua, Shehu Yar’adua da amaryarsa Yacine Sheriff, wacce diya ce ga Hon. Mohammed Nur Sheriff.

Tuni hadaddun hotunan Shehu da zukekiyar amaryarsa suka bayyana a shafukan soshiyal midiya inda yan uwa da abokan arziki suka dukufa shirye-shiryen bikin.

Shehu Yar'adua da amaryarsa
Hadaddun Hotunan Shehu Yar’Adua Da Amaryarsa Yacine Sheriff Yayin Da Suke Shirin Shiga Daga Ciki Hoto: blackswansazy
Asali: Instagram

A cikin hotunan da shafin blackswansazy ya wallafa a Instagram, an gano Shehu ya yi shiga irin ta angwanan Turawa na kwat da wando yayin da ita kuma Amarya Yacine ta sanya doguwar farar riga irin ta amare sannan ta yane kanta da mayafi.

Kara karanta wannan

Biki Ake Na Manya: Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu

Shehu ya kasance rike da hannun amaryar tasa yana yi mata kallo mai cike da shauki da kauna inda ita kuma ta juya masa baya rike da furen soyayya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli hotunan a kasa:

Shehu Yar'adua da amaryarsa
Hadaddun Hotunan Shehu Yar’Adua Da Amaryarsa Yacine Sheriff Yayin Da Suke Shirin Shiga Daga Ciki Hoto: blackswansazy
Asali: Instagram

Shehu Yar'adua da amaryarsa
Hadaddun Hotunan Shehu Yar’Adua Da Amaryarsa Yacine Sheriff Yayin Da Suke Shirin Shiga Daga Ciki Hoto: blackswansazy
Asali: Instagram

Tun farko dai, mun kawo cewa Abokan marigayi tsohon shugaban kasan Najeriya Umaru Musa 'Yar' Adua na shirye-shiryen daura auren dan gidan marigayin.

A cewar majiyoyi, kwamitin tsare-tsare karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Alhaji Yayale Ahmed, sun yi taro a ‘yan makonnin da suka gabata a gidan uwargidan tsohon shugaban kasar domin shirye-shiryen auren a Maiduguri.

Shehu dan shekara 29, ya samu digirin sa na farko a fannin tattalin arziki daga makarantar kasuwanci ta Schellhammer da ke kasar Spain, sannan ya yi digiri na biyu a fannin hulda da kasashen duniya daga jami’ar Webster da ke kasar Netherlands.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

Amaryar, Yacine, mai shekaru 22, ta yi digirin farko a fannin kula da baki daga Jami’ar Surrey da ke Birtaniya.

Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu

A wani labarin kuma, kamar yadda labari ya karade lungu da kaso na Najeriya, diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Fatima Kashim Shettima na shirin shiga daga ciki.

Za a dai kulla auratayya a tsakanin Fatima da masoyinta Sadiq Ibrahim Bunu a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli.

Tuni dai aka fara bude taro da kasaitaccen liyafa ta Dina inda amarya da ango suka gaji da kyau tare da fitowa shar da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel