Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu

Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu

  • Tuni aka fara shagulgulan bikin diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima
  • Fatima Kashim Shettima da angonta Sadiq Bunu sun bayyana a kasaitaccen liyafar Dina da aka shirya na bikinsu
  • Amarya ta gaji da haduwa inda ta sanya hadaddiyar doguwar riga na amare yayin da ango ya ci yadi dinkin babbar riga

Kamar yadda labari ya karade lungu da kaso na Najeriya, diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Fatima Kashim Shettima na shirin shiga daga ciki.

Za a dai kulla auratayya a tsakanin Fatima da masoyinta Sadiq Ibrahim Bunu a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli.

Fatima Shettima da angonta
Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu Hoto: blackswansazy
Asali: Instagram

Sai dai kuma kamar yadda aka saba bisa al’adan bikin ‘ya’yan manya a Najeriya, tun a makon nan ne aka fara gudanar da shagulgulan bikin.

Kara karanta wannan

Hadaddun Hotunan Shehu Yar’Adua Da Amaryarsa Yacine Sheriff Yayin Da Suke Shirin Shiga Daga Ciki

Tuni dai aka fara bude taro da kasaitaccen liyafa ta Dina inda amarya da ango suka gaji da kyau tare da fitowa shar da su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A daya daga cikin bidiyoyin da shafin blackswansazy ya wallafa a Instagaram, an gano amarya sanye da wata hadaddiyar doguwar riga fara irin ta amare kanta yane da lullubi inda ta tsaya ana ta daukarta hadaddun hotuna.

Bayan nan amaryar ta kuma sauya kaya zuwa wata doguwar riga da ta sha banban da wacce ta fara sakawa sannan kuma a wannan karon, kallabi ta daura a kanta. Shi kuma angon ya kasance sanye da bakin yadi dinkin babbar riga da hula zannar bukar.

An gano su suna rawa tare da rera sautin wakar da ke tashi a dakin taron yayin da yan uwa da abokan arziki ke taya su murnar cikar wannan buri nasu.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

Kalli bidiyoyin a kasa:

Hotunan tsohuwar matar gwamna tare da kyakyawan matashi sharaf da tayi wuff da shi

A wani labari na daban, Hajiya Hauwa, tsohuwar matar marigayi tsohon gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai, ta bayyana a kyawawan hotuna tare da matashin da tayi wuf da shi, Halliru Saad Malami.

Mai daukar hoto Nexus ne ya zuba hotunan a shafinsa na Instagram a ranar Talata, 12 ga watan Yulin 2022.

Hajiya Hauwa ta auri Malami, wanda shine CEO na ITBAN Global Resources Ltd a shekarar 2019, shekaru biyu bayan mutuwar Suntai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel