Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi APC a 2023 don samun damar ci gaba da ganin irin ayyukana

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi APC a 2023 don samun damar ci gaba da ganin irin ayyukana

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya da su zabi jam'iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa nan kusa
  • Shugaban kasan ya sha bayyana irin ayyukan alherin da ya yiwa Najeriya, inda yace akwai bukatar ci gaba da yin su
  • Jam'iyyar APC ta tsayar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda zai yiwa jam'iyyar takarar shugaban kasa a 2023

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar kasar nan da su zabi APC a zabe mai zuwa domin tabbatar da dorewar harkokin siyasa, da kwanciyar hankali a kasar da ma yankin yammacin Afrika, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya bayyana haka ne a yau Juma’a a lokacin da yake karbar tawagar daga jihar Nasarawa karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Sule a fadar gwamnati da ke Abuja, a cewar sanarwar da fadarsa ta fitar.

Kara karanta wannan

2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

Buhari ya roki 'yan Najeriya su zabi Tinubu
Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi APC don ci gaba da shan jar miyar da nake baku | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce zabukan da aka yi a jihohin Anambra, Ekiti da Osun sun tabbatar da kudurin gwamnatinsa na ganin an gudanar da sahihin zabe ba tare da tashin hankali ba.

Buhari, shaida wa tawagar cewa, dokar zabe da ya sanya wa hannu a farkon wannan shekara wata shaida ce ta cika kudurin gwamnati da kuma jajircewarta wajen bin ka’idojin mulki da na doka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake bayyana burinsa na nan gaba, Punch ta ruwaito Buhari na cewa:

“Muradina ga al’ummarmu shi ne zaben 2023 ya kamata hukumar zabenmu ta fito karara ta fara nuna karfinta wajen gudanar da zabubbuka masu inganci, sahihai kuma ba tare da tashin hankali ba.
‘’ Zaben da ke tafe zai ba mu damar gamsar da jama’a kan bukatar ci gaba da baiwa jam’iyyarmu damar daurawa kan nasarorin da muka samu a cikin shekaru 7 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

“Gwamnati da al’ummar Jihar Nasarawa, kamar yadda suka saba, suna da rawar da za su taka wajen dawo da jam’iyyarmu kan karagar mulki a zaben 2023, domin samar da hanyar bunkasa zamantakewa da tattalin arziki da ci gaba.
"Wannan ba kawai yana da mahimmanci ga Najeriya NE kadai ba har ma da yankin yammacin Afirka."

Buhari, wanda ya ce Nasarawa ta kasance abin da yake so a zuciyarsa, ya bayyana jihar a matsayin alama ta fata da jajircewa a kokarin da ake na tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya.

Buhari ya shiga wata ganawa da manyan jiga-jigan jam'iyyar APC

A wani labarin, a halin yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari na can na ganawa da wata tawaga ta jiga-jigan jam'iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, rahoton Punch.

Tawagar wacce ta kunshi shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase, Kashim Shettima, da sauran manyan ‘ya’yan jam’iyyar, ya zo ne domin ganawa da Buhari da misalin karfe 03:00 na yamma a yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Da na sha kaye a zabe inda Buhari bai rattaba hannu kan dokar zabe ba - Adeleke

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole, tsohon ministan noma, Audu Ogbe da tsohon babban hafsan sojin sama Air Marshall Sadiq Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel