Hotuna: Zukekiyar diyar Kashim Shettima, Fatima Shettima zata amarce, katin gayyata ya fito

Hotuna: Zukekiyar diyar Kashim Shettima, Fatima Shettima zata amarce, katin gayyata ya fito

  • Alkawarin masoya biyu, Fatima Kashim Shettima tare da masoyinta, Sadiq Ibrahim Bunu, ya kusa cika, hotunan kafin aure sun fito
  • Tuni dai shirin auren masoyan ya kankama wanda za a yi a ranar 30 ga watan Yulin 2022 a garin Maiduguri na jihar Borno
  • Kyawawan hotunan Fatima da angonta Sadiq sun bayyana yayin da katin gayyatar bikin 'yan gatan ya fito das

Maiduguri, Borno - Fatima Kashim Shettima, kyakyawar diyar 'dan takarar mataimakin shugaban kasan Najeriya, Kashim Shettima na jihar Borno, ta shirya tsaf domin amarcewa da zukeken angonta mai kyau.

Fatima da kyakyawan angonta mai suna Sadiq Ibrahim Bunu, zasu zama daya kuma alkawarin masoyan zai cika a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli 2022 a garin Maiduguri dake jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

Ftatima Kashim
Hotuna: Zukekiyar diyar Kashim Shettima, Fatima Shettima zata amarce, katin gayyata ya fito. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tuni kyawawan hotunan Fatima da zukeken angonta suka fara yawo yayin da shirye-shiryen kasaitaccen aurensu yayi nisa.

A halin yanzu, katin gayyata na wannan bikin 'yan gatan ya fito kuma ya fara karade kafafen sada zumuntar zamani.

Fatima Kashim
Hotuna: Zukekiyar diyar Kashim Shettima, Fatima Shettima zata amarce, katin gayyata ya fito. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Fatima Kashim
Hotuna: Zukekiyar diyar Kashim Shettima, Fatima Shettima zata amarce, katin gayyata ya fito. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Fatima Kashim
Hotuna: Zukekiyar diyar Kashim Shettima, Fatima Shettima zata amarce, katin gayyata ya fito. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Hotunan tsohuwar matar gwamna tare da kyakyawan matashi sharaf da tayi wuff da shi

A wani labari na daban, Hajiya Hauwa, tsohuwar matar marigayi tsohon gwamnan jihar Taraba, Danbaba Suntai, ta bayyana a kyawawan hotuna tare da matashin da tayi wuf da shi, Halliru Saad Malami.

Mai daukar hoto Nexus ne ya zuba hotunan a shafinsa na Instagram a ranar Talata, 12 ga watan Yulin 2022.

Hajiya Hauwa ta auri Malami, wanda shine CEO na ITBAN Global Resources Ltd a shekarar 2019, shekaru biyu bayan mutuwar Suntai.

Kara karanta wannan

Auren manya: Ana babban shiri, dan tsohon shugaban kasa 'Yar Adua zan angwance

Asali: Legit.ng

Online view pixel