Shugabannin NNPP sun mutu wajen dawowa taron siyasa, Kwankwaso ya yi magana

Shugabannin NNPP sun mutu wajen dawowa taron siyasa, Kwankwaso ya yi magana

  • Jam’iyyar NNPP ta na jimamin mutuwar wasu shugabannin jam’iyyar NNPP a hadarin mota
  • Jagororin jam’iyyar hamayyar sun gamu da hadarin mota a hanyar su ta komawa Neja daga Abuja
  • Rabiu Musa Kwankwaso ya fitar da jawabi ta bakin Hadiminsa, ya na ta’aziyyar rashin da aka yi

Niger - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani yayin da ya samu labarin jam’iyyar NNPP ta rasa wasu daga cikin shugabanninta a sakamakon hadarin mota.

A wata sanarwa da Hadimin ‘dan takaran shugaban kasar ya fitar a Facebook, an ji cewa jagororin jam’iyyar NNPP sun rasa ransu da suka yi hadari a hanya.

Kamar yadda Muyiwa Fatosa ya bayyana, hadarin ya auku ne a kan titin Suleja-Lambata a jihar Neja.

Fatosa wanda yake magana da yawun Rabiu Kwankwaso, ya ce wadanda suke cikin motar sun gamu da mummunan rauni, wasunsu suka ce ga garinku nan.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

Mutane hudu sun cika

Kamar yadda jawabin da aka fitar ya nuna, wadanda suka riga mu gidan gaskiya su ne shugabannin jam’iyyar NNPP na kananan hukumomin Aagie da Kacha.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika akwai shugaban matasa na jam’iyyar NNPP a garin Gbako duk a Neja, da direbansu.

Wasu sun samu rauni

Da yake bayani a shafinsa na Facebook, Ahmed Aliyu Lanle ya ce shugabannin jam’iyyar adawar na kananan hukumomin Gbako, Edati, da Lapai sun samu rauni.

Wadannan mutane su na kan hanyarsu ta komawa gida ne abin ya faru a daidai yankin Old Gawu zuwa Lambata, bayan sun baro garin Abuja a makon nan.

A yanzu wadannan Bayin Allah su na jinya a asibiti, har zuwa lokacin da ake sa ran samun sauki.

Jawabin Kwankwaso

“Na ji bakin cikin samun labarin mutuwar wasu shugabannin reshen kananan hukumomi na jam’iyyarmu ta NNPP a jihar Neja.”

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Sanata da tsohon Minista sun shiga NNPP a Jihohin Taraba da Bauchi

“Bayanan da na samu shi ne mamatan sun rasu ne a wani mummunan hadarin mota a titin Old Gawu, su na hanyar komawa gida.”

-Rabiu Musa Kwankwaso

‘Dan takaran shugaban kasar ya yi addu’ar samun Aljannah ga wadanda suka rasu, tare da rokon Ubangiji ya hana aukuwar irin wannan musiba a nan gaba.

Sule Lamido da 2023

Ku na da labari tsohon Minista kuma tsohon gwamnan jihar Jigawan ya yi kira ga Nyesom Wike, ya kuma soki masu magana saboda PDP ta tsaida yaronsa.

Tun da 'dansa yana takara, Sule Lamido ya ce babban laifinsa a Jigawa shi ne haihuwa. Sannan ya yi magana a game da NNPP da aka farfado da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel