Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya gabatar da Isaac Idahosa a babban dakin taro na ICC da ke garin Abuja
  • Sanata Kwankwaso ya nuna a shirya suke da su magance matsalolin da Najeriya ta ke fama da su
  • ‘Dan takara na NNPP ya kara yin bayani a game da dalilinsa na daukar Idahosa su yi takara tare

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ta kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da Isaac Idahosa a matsayin abokin tafiyarsa.

Punch ta ce Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da Bishof Isaac Idahosa ne a babban dakin taro na ICC da ke Abuja a ranar Litinin 18 ga watan Yuli 2022.

Da yake jawabi a wajen taron, ‘dan takarar shugaban kasar a zaben 2023 ya bayyana cewa Najeriya ta shiga mawuyacin hali, ta na bukatar wanda zai ceto ta.

Kara karanta wannan

Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

A cewar Rabiu Kwankwaso, rashin fahimtar yadda za a jagoranci al’umma masu addinai da kabilu barkatai, ya sa Muhammadu Buhari ya lalata kasar nan.

Kwankwaso ya ce rashin sanin aiki da rashin tausayi sun yi wa mutanen Najeriya mummunar illa. Haka zalika an samu karuwar rabuwar kai tsakanin jama'a.

An rahoto ‘dan takaran yana zargin gwamnati mai-ci da zama sanadiyyar ta’azzarar rashin tsaro, tsadar rayuwa, rashin aikin yi da tabarbarewar ilmi da sauransu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwankwaso ya kaddamar da Idahosa
Rabiu Kwankwaso da Isaac Idahosa Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook
“Mu na zaune a kasar da ake watsi da wadanda matsalar rashin tsaro ta shafa, ana zarginsu da karya ko zuzuta lamarin, ko laifin yin duka.”
“Mu na zaune a kasar da ake zargin wadanda ba su da aikin yi da cewa malalata ne.”
“Ana rufe jami’o’i da sauran makarantu na watanni, amma shugabanni su na kashe miliyoyin daruruwa wajen sayen fam domin yin takara.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Abin Da Yasa Na Zabi Bishof Idahosa Matsayin Abokin Takara Na

- Rabiu Kwankwaso

An kama hanyar kawo gyara

A jawabinsa, Kwankwaso ya ce daukar abokin takara shi ne matakin farko na kawo gyara, ya ce shi da Idahosa za su dinke Najeriya daga halin da ta ke ciki.

‘Dan takaran ya kara jaddada cewa sai da aka tantance mutane kusan 20, sannan aka kai ga dauko Bishof Idahosa wanda limami ne a cocin God First Ministry.

“Mutum ne wanda ya yarda da cigaban Najeriya, na yi imani za mu iya yin aiki tare cikin gaskiya, domin magance matsalolin da aka jefa Najeriya a ciki.”

- Rabiu Kwankwaso

Dalilin dauko Idahosa a NNPP

An ji labari cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya ce tsabar amincinsa ne ya sa ya dauki Bishop Isaac Idahosa ya zama mataimakinsa karkashin inuwar NNPP a 2023.

Sanata Kwankwaso ya ce ya natsu ya yi rairaye da tankade kafin ya zabo Idahosa cikin sunayen nagartattun mutanen da suka cancanci yin takara tare da shi.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel