Tashin hankali: Sabuwar cuta ta bullo a wata makaranta, mutum 10 sun jikkata, 1 ya mutu

Tashin hankali: Sabuwar cuta ta bullo a wata makaranta, mutum 10 sun jikkata, 1 ya mutu

  • An samu bullar wata sabuwar cuta a jihar Delta, ta kwantar da dalibai 10, ta kashe wata daliba daya
  • Hukumomin wata makaranta da ke yankin Agbor sun bayyana yadda wani kamfanin iskar gas ke gurbata yankin
  • Ba sabon abu bane samun gurbatar yanayi ya kawo cuta a yanzunan da mutane ke zauna a sassa daban-daban na duniya

Asaba, jihar Delta - An kwantar da mutane goma a asibiti kana wani ya mutu daga wata nau'in cuta da ta bulla a Boji-Boa na jihar Delta.

Cutar dai ta dumfari daliban makarantar Mary Mount College ne, inda ta tabbata a jikin mutum biyar. An ce daga alamar ta akwai suma da faduwa haka siddan.

Jaridar Leadership ta bibiyi lamarin a ma'aikatar lafiya ta jihar, inda ta tabbatar da cewa ana kula da mutum hudu da suka rayu a wani asbitin gwamnati da ke jihar.

Kara karanta wannan

Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

Hakazalika, rahoton ya ce an garkame makarantar har sai lamurra sun lafa.

Cuta ta bullo a jihar Delta
Tashin hankali: Sabuwar cuta ta bullo a wata makaranta, mutum 10 sun jikkata, 1 ya mutu | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bincike ya nuna cewa daya daga cikin daliban da abin ya shafa ta mutu makonni da suka gabata bayan da iyayenta suka kai ta asibiti don neman magani.

An kai dalibai hudu daga cikin 10 da suka kamu da cutar zuwa asibitin St John’s a yankin Agbor, a jihar, yayin da iyayen sauran daliban suka kai yaransu zuwa asibitoci daban-daban.

Sister Kuna Yakubu Ola na Mary Mount College, Agbor da kuma sakatariyar makarantar, Mrs Rita Otuasia, sun tabbatar da faruwar lamarin.

Hukumar makarantar ta ce nan da nan ta sanar da iyayen yara da jami'an hukumar lafiya lokacin da ta lura da alamar bullar cutar.

Makarantar ta ce tana zargin wata masana'antar iskar gas da ke kusa da wurin ta kawo cutar.

Kara karanta wannan

Karyewar Crypto: Shugaban Binance da wasu attajiran Crypto 10 da ke ganin karayar arziki

Jami’an makarantar sun ce sun dade suna rokon mai kamfanin da ya kaura domin lafiyar al'umma, rahoton Daily Sun.

Sakataren dindindin a ma’aikatar ilimi ta bai daya da sakandare ta jihar Mista Augustine Oghoro ya ce ma’aikatarsa na hada kai da ma’aikatar lafiya domin gano musabbabin cutar da kuma nemo maganinta.

Ta kuma bukaci wakilan kwalejin da su baiwa kwamitin gano bullar cutar bayanan daliban da sunayen iyayensu da abokan huldar su ta yadda za a iya samun damar sanin irin bulla da shawo kan cutar a nan gaba.

Sabuwar cuta da ke kumbura kafafu ta bulla a Bauchi, ta kwantar da mutane 10

A wani labarin, an tabbatar da ɓullar wata sabuwar cuta wacce ke sanya kumburin ƙafafuwa a ƙauyen Bura, ƙaramar hukumar Kirfi da ke jihar Bauchi, kuma ya zuwa yanzu mutane 10 sun kamu da wannan cuta.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga babban shugaban hukumar kiwon lafiya daga matakin farko ta jihar (BASPHCDA), Dr Rilwanu Mohammed, ya yin tattaunawa da manema labarai a ranar bukin cututtukan da aka yi watsi da su na duniya (NTA) a shekarar 2021, da ya gudana a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, Jarumar fim mai shekaru 52

Rilwanu Mohammed ya ce: "A yammacin ranar Lahadi, mun samu rahotanni kan cewar akwai cutar da ta ɓulla mai kumbura ƙafafuwa, kuma ya zuwa yanzu mutane 10 sun kamu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel