Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

  • Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewa masu Yammacin Najeriya da suka sha fama da hare-haren 'yan bindiga
  • A makon nan ne rahotanni suka karade kasa cewa,wata masarauta a jihar Zamfara ta nada kasurgumin dan bindiga sarauta
  • A bangare guda, an samu mummunan harin 'yan bindiga a wani yankin jihar Kaduna; Arewa maso Yammacin Najeriya

Jihar Zamfara - Rahoton jaridar Vangurad ya ce, sama da ‘yan bindiga 100 a ranar Asabar sun halarci bikin nadin sarautar kasurgumin shugabansu mai suna Ada Aleru a matsayin Sarkin Fulani, wanda Sarkin Yandoto ya nada.

Rahotanni da dama sun ruwaito cewa, masarautar ta nada kasurgumin dan bindigan ne daidai lokacin da jihar ke ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna A Jihar Filato

Yadda aka naɗa Aleru sarauta a Zamfara
Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara | Hoto: channestv.com
Asali: UGC

Sai dai, wata majiya da ta zanta da manema labarai ta shaida dalilin da yasa sarkin ya nada dan bindigan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar majiyar yayin da take bayyana yadda lamarin ya faru:

“’Yan bindigar na tafiya ne a kan babura ba tare da bindigoginsu ba. Kwarya-kwaryan biki ne kawai da ya samu halartar wasu tsirarun mutane.
“Sarkin Yandoto, Alhaji Garba Marafa, ya baiwa fitaccen dan bindigan nan da yayi ta’addanci a jahohin Zamfara da Katsina sarautar Sarkin Fulani saboda a shirye yake ya kama kansa ya kuma rungumi zaman lafiya.
“A wani taro da aka yi, Ada Aleru ya amince da daina kai hare-hare kan al’ummomi da kauyukan masarautar. Ya kuma amince da barin mutane su je gonakinsu.
"Wannan ya sanya masarautar ta ba Aleru sarauta domin ya taimaka wajen ganin an dawo da zaman lafiya a masarautar."

Kara karanta wannan

Zamfara: Hatsabibin Dan Bindiga Da Ya Dade Yana Addabar Mutane Zai Zama Sarki

Wani rahoton Daily Trust ya zayyano irin manya-manyan ayyukan ta'addanci da Aleru ya jagoranta a yankunan jihohin Katsina da Zamfara.

Mummunan hari a Kaduna

A bangare guda, wasu ‘yan bindiga da dama sun fito daga dajin Zamfara sun tsallaka zuwa Tudunwada-Sabon Layi da ke yammacin Birnin-Gwari a Jihar Kaduna, inda suka kashe wani dan unguwar tare da raunata uku a wani mamaya da suka yi.

Wani jami’in kungiyar tsaro da kyakkyawan shugabanci na Birnin-Gwari ya bayyana cewa:

“A yanzu haka suna ta kwasar ganima a Ganun-Gari daura da Dawakin Bassa bayan yiwa makwabciyarta Unguwar Baki fashi.
“’Yan bindigar sun yi awon gaba da shanu tare da kwashe kayan abinci a Unguwar Baki.
“Ba a san adadin wadanda suka mutu ba a halin yanzu. Amma ana sa ran ‘yan bindigan za su dawo ta wannan hanya (Tudunwada-Sabon Layi) zuwa maboyar su da ke Zamfara.
“An kashe mutum daya, wasu uku kuma sun jikkata a Ganun-Gari. Yanzu haka ‘yan bindigar suna Dawakin Bassa. Ana ci gaba da samun harbe-harbe mai tsanani a halin yanzu. Ana jin karar harbin bindigogi a kauyukan Unguwar zakara da Kubo.

Kara karanta wannan

Kotu ta wanke wadanda suka gudanar da zanga-zangar cin mutuncin Buhari a Kogi

“’Yan bindigar za su koma sansaninsu bayan sun kai farmaki a Dawakin Bassa ta hanyar da suka bi da fari.”

Zamfara: Hatsabibin Dan Bindiga Da Ya Dade Yana Addabar Mutane Zai Zama Sarki

A tun farko, idan har gwamnatin Jihar Zamfara bata dauki matakin hana wa ba, an kammala shiri don nada hatsabibin dan bindiga, Adamu Aleru, a matsayin Sarkin Fulani a masarautar Yandoton Daji a ranar Asabar.

Majiyoyi daga yankin wadanda suka nemi a boye sunansu saboda tsaro, sun shaidawa Premium Times cewa an yanke shawarar nada dan ta'addan sarauta ne don samun dawamammen zaman lafiya a masarautun Tsafe da Yandoton Daji da wasu yankunan jihohin Zamfara da Katsina, da Aleru da makarrabansa suka saba kai hari.

Yandoton Daji na cikin sabbin masarautu biyu da gwamnatin Jihar Zamfara ta kirkira a watan Mayu. An kirkire ta ne daga masarautar Tsafe. Sarkin Yandoton shine Aliyu Marafa.

Kara karanta wannan

Don Tinubu ya zabi Musulmi: Jarumin Nollywood Kenneth Okonkwo ya fice daga APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel