Sabuwar cuta da ke kumbura kafafu ta bulla a Bauchi, ta kwantar da mutane 10

Sabuwar cuta da ke kumbura kafafu ta bulla a Bauchi, ta kwantar da mutane 10

- Rahotannin daga jihar Bauchi sun bayyana cewa an samu bullar wata sabuwar cuta mai kumbura kafafu

- Shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko na jihar Bauchi, Dakta Rilwanu Mohammed, ya tabbatar da hakan

- A cewar kwamishinan, sabuwar cutar ta kwantar da mutane goma a kauyen Bura da ke karamar hukumar Kirfi

An tabbatar da ɓullar wata sabuwar cuta wacce ke sanya kumburin ƙafafuwa a ƙauyen Bura, ƙaramar hukumar Kirfi da ke jihar Bauchi, kuma ya zuwa yanzu mutane 10 sun kamu da wannan cuta.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga babban shugaban hukumar kiwon lafiya daga matakin farko ta jihar (BASPHCDA), Dr Rilwanu Mohammed, ya yin tattaunawa da manema labarai a ranar bukin cututtukan da aka yi watsi da su na duniya (NTA) a shekarar 2021, da ya gudana a ranar Litinin.

Rilwanu Mohammed ya ce: "A yammacin ranar Lahadi, mun samu rahotanni kan cewar akwai cutar da ta ɓulla mai kumbura ƙafafuwa, kuma ya zuwa yanzu mutane 10 sun kamu.

"Na umurci sashen dakile yaduwar cututtuka da ke a hukumar da ya ziyarci ƙauyen domin yin bincike kan wannan sabuwar cuta."

Ya kara da cewa: "Muna hasashen cewa kwayar cutar "onchocerciasis" ko kuma "lymphatic filariasis" ce ta kama mutanen la'akari da cewa karamar hukumar na fama da cututtukan daji. Da zaran mun samu tabbacin cutar da ke damun su, za mu dauki matakin da ta dace don dakile yaduwar cutar."

Sabuwar cuta da ke kumbura kafafu ta bulla a Bauchi, ta kwantar da mutane 10
Sabuwar cuta da ke kumbura kafafu ta bulla a Bauchi, ta kwantar da mutane 10
Asali: Twitter

Dangane da bukin ranar NTDs, shugaban hukumar BASPHCDA ya ce mafi akasarin cututtukan da suka shafi muhalli da daji suna zuwa ne sakamakon rashin tsabtataccen ruwan sha, inda sama da mutane miliyan 1 ne suke fama da ire Iren wadannan cutukan.

Cututtukan muhallin da aka fi yin biris da su, sun hada da: Onchocerciasis, lymphatic filariasis, soil-transmitted helminths, trachoma, schistosomiasis, Buruli ulcer, snake bite, leprosy, human African trypanosomiasis, Guinea worm, yaws da kuma loiasis, Sannan ya ce za a iya magance wadannan cututtukan ne ta hanyar tsaftar muhalli da ta jiki.

Ya yi nuni da cewa ya zuwa yanzu, jihar Bauchi na fama da cutar "Onchocerciasis" a kananan hukumomi 12; "lymphatic filariasis" a kananan hukumomi 11; "Schistosomiasis" a kananan hukumomi 16; "Trachoma" a kananan hukumomi 2 sai kuma "Guinea worm" wacce tuni aka kawo karshen ta a fadin Nigeria.

Rilwanu Mohammed ya kara da cewa sashen kula da kuma dakilewa da kuma gwamnatin jihar na aiki kafada da kafada da asusun UNICEF da kuma wata kungiya mai rajin taimakawa marasa galihu (MITOSATH).

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel