Karfin hali: An cafke wani dan shekara 60 da ya tsere daga gidan yarin Kuje a Kaduna

Karfin hali: An cafke wani dan shekara 60 da ya tsere daga gidan yarin Kuje a Kaduna

  • Jami'an 'yan sandan jihar Kaduna sun yi nasarar cafke wani mutumin da ya tsere daga gidan yarin Kuje makon jiya
  • A kwanakin nan ne aka kai mummunan hari cibiyar kula da gyaran hali da ke Kujer, lamarin da ya girgiza al'umma
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da gano fursunonin da suka tsere daga gidan gyaran halin a sassan kasar nan

Jihar Kaduna - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun kama daya daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje, inji rahoton jaridar Punch.

Kakakin rundunar, Mohammed Jalige, ya bayyana kama wani Ali Shuaibu dan shekara 60, dan asalin jihar Kano, a matsayin wanda aka sake kamawa a Kaduna ranar Asabar yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa mahaifarsa (Kano).

Yadda aka kama fursunan da ya tsere daga Kuje a Kaduna
Karfin hali: ‘Yan sanda sun kama wani dan shekara 60 da ya tsere daga gidan yarin Kuje a Kaduna | Hoto: thenationonlioneng.net
Asali: UGC

A cewarsa, wanda ake zargin ya bayyana cewa yana daga cikin fursunonin da suka tsere a harin da aka kai a cibiyar gyaran hali ta Kuje.

Kara karanta wannan

Fashin magarƙama: An kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje ɗauke da kayan laifi a Katsina

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yekini Ayoku, ya bayar da umarnin bincike kafin mika shi ga hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya domin a tura shi wurin da ya dace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar wani yanki na sanarwar kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

“Wanda ake zargin Ali Shuaibu dan shekara 60 kuma dan asalin jihar Kano, jami’an ‘yan sanda ne suka kama shi a wani wuri a Kaduna, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kano bisa samun bayanan sirri.
“Wanda ake zargin yayin binciken farko ya bayyana cewa yana cikin fursunonin da suka tsere a harin da aka kai a tsakiyar cibiyar tsaro ta Kuje.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Kaduna CP Yekini A. Ayoku psc (+), mni ya bayar da umarnin a aiwatar da ka’idojin da suka dace kafin mika wanda ake zargin ga hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya domin a tura shi wurin da ya dace.

Kara karanta wannan

Bayan Kama Dan Boko Haram a Nasarawa, Yan Sanda Sun Sake Kamo Wani Cikin Fursunoni Da Ya Tsere Daga Kuje

“Ya kuma umurci jami’an da kada su yi kasa a gwiwa a kokarinsu na magance duk wani nau’in laifuffuka da ta'addanci a duk sassan jihar.”

Harin gidan yarin Kuje: Yan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere a jihar Ogun

A wani labarin, rundunar yan sanda a Ogun a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli, ta bayyana cewa ta kama wani da ya tsere daga gidan yarin Kuje, Yakubu Abdulmumuni, a yankin Sango-Ota da ke jihar.

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a cikin wata sanarwa da manema labarai a Ota, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin, jaridar Premium Times ta rahoto.

Mista Oyeyemi ya yi bayanin cewa an kama Abdulmumuni mai shekaru 28 ne bayan bayanai da jami’an yan sanda a hedkwatar rundunar da ke Sango-Ota, suka samu cewa an gano fursunan a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel