Nada dan bindiga sarauta: Har yanzu Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba - Masari

Nada dan bindiga sarauta: Har yanzu Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba - Masari

  • Masarautar 'Yandoton daji dake jihar Zamfara ta nadawa rikakken dan ta’adda ,Ado Aleiro, sarautar Sarkin Fulani
  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya ce har yanzu gwamnatinsa bata yafewa Aleiro kashe mutanen da ya yi a Kadisau da Faskari ba
  • Gwamnatin Katsina ta ce ta cika da mamakin jin cewa dan ta’addan da take nema ruwa a jallo ya samu sarauta a Zamfara

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa har yanzu bata yafewa Ado Aleiro, dan bindigar da take nema ruwa a jallo ba.

A ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli ne aka yiwa Aleiro wanda ya kasance rikakken dan ta'adda nadin sarautar Sarkin Fulani a masarautar 'Yandoton daji dake jihar Zamfara.

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya shaidawa sashin BBC Hausa cewa sun kadu matuka da jin labarin nadin sarautar da aka yiwa Aleiro.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

Masari ya bayyana cewa har gobe kallon dan ta’adda suke yiwa Ado Aleiro koda kuwa ya daina aikata ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara.

Aminu Bello Masari
Nada dan bindiga sarauta: Har yanzu Katsina ba ta yafe wa Ado Aliero ba - Masari Hoto: Arise tv
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa ya yi kokarin tuntubar takwaransa na jihar Zamfara, Gwamna Bello Matawalle tun bayan faruwar al’amarin, amma bai samu damar tattaunawa da shi ba.

Hakazalika, Masari ya ce har gobe gwamnatinsa na nan a kan bakarta ta neman dan ta’addan ido rufe kan zarginsa da ake da halaka mutanen Kidasau da na Faskari.

Zamfara: Matawalle Ya Dakatar Da Sarkin Da Ya Nada Gogarmar Dan Bindiga Sarautar Sarkin Fulani

A baya mun ji cewa, gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Birnin Ƴandoto, Aliyu Marafa saboda naɗa shugaban yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Adamu Aliero-Yankuzo, Sarkin Fulani, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ganduje ya haramta amfani da Adaidaita sahu da daddare a Kano

Matakin da masarautar ta dauka na nada ɗan bindigan sarauta ya janyo cece-kuce inda da dama suka soki naɗin sarautar da aka yi wa ɓata garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel