An Yi Awon Gaba Da Shugaban CAN Da Abokin Aikinsa A Kaduna

An Yi Awon Gaba Da Shugaban CAN Da Abokin Aikinsa A Kaduna

  • Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace shugaban kungiyar CAN na Jema'a da abokin aikinsa
  • An sace Rabaran Fada John Cheitnum da Rabaran Fada Donatus Cleopas a gidan saukan fastoci da ke Christ the King Catholic Church, Yadin Garu, Lere
  • Emmanuel Okolo, na cocin na yankin, ya bukaci addu'a daga mutane don ganin an sako limaman cocin, ya kuma bukaci mutane su guji daukan doka a hannunsu

Lere, Kaduna - Cocin Darikar Katolika ta Kafanchan, Jihar Kaduna, ta sanar da sace Rabaran Fada John Cheitnum da Rabaran Fada Donatus Cleopas, rahoton Daily Trust.

Chietnum shine shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya wato CAN, reshen karamar hukumar Jama'a ta Jihar Kaduna.

Taswirar Jihar Kaduna.
An Yi Awon Gaba Da Shugaban CAN Da Abokin Aikinsa A Kaduna. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kara yin garkuwa da limaman cocin Katolika a jihar Kaduna

Cikin wata sanarwa, shugaban cocin reshen Jema'a, Rabaran Fada Emmanuel Okolo, ya ce an sace limaman cocin biyu ne a ranar Juma'a a gidan fastoci da ke Christ the King Catholic Church, Yadin Garu, karamar hukumar Lere.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna sanar muku da sace biyu cikin limaman mu: Rabaran Fada John Cheitnum da Rabaran Fada Donatus Cleopas.
"Abin bakin cikin ya faru ne misalin karfe 5.45 na yammacin ranar 15 ga watan Yulin 2022.
"Ya faru ne jim kadan bayan limaman biyu, wadanda ke kan hanyarsu zuwa wani taro, sun isa masaukin fastoci da ke Christ the King Catholic Church, Yadin Garu a karamar hukumar Lere, Jihar Kaduna," in ji shi.

Cocin ta nemi mutane su taya ta da addu'an ganin an sako limaman cocin

Okolo, ya nemi addu'a domin ganin an saki su a wuri yayin da ya gargadi mazauna yankin game da daukan doka a hannunsu.

Kara karanta wannan

Kotu ta wanke wadanda suka gudanar da zanga-zangar cin mutuncin Buhari a Kogi

Ya ce cocin za ta yi amfani da duk wani hanya da doka ta halasta domin ganin an sako su cikin lafiya.

Masu Garkuwa Sun Sace Fasto a Cocinsa

A wani rahoton, wasu yan bindiga da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun sace faston cocin Deeper Life a garin Irese da ke karamar hukumar Akure ta Kudu na jihar Ondo mai suna Ogedengbe.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 10 ga watan Mayu a harabar cocin kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wani mamba na cocin wanda ya tabbatar da sace faston ya ce wadanda suka sace shi sun taho ne cikin bakar mota kirar Toyota Corolla.

Asali: Legit.ng

Online view pixel