Labari da Dumi-Dumi: Masu Garkuwa Sun Sace Fasto a Cocinsa
- 'Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kutsa coci sun yi awon gaba da fasto a karamar hukumar Akure ta Kudu jihar Ondo
- Wani shaidan gani da ido ya ce yan bindigan sun shigo harabar cocin ne cikin mota mai launin baki kirar Toyota Corolla
- Mai magana da yawun rundunar yan sandan na jihar Ondo ASP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da sace faston yana mai cewa an fara bincike
Wasu yan bindiga da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun sace faston cocin Deeper Life a garin Irese da ke karamar hukumar Akure ta Kudu na jihar Ondo mai suna Ogedengbe.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 10 ga watan Mayu a harabar cocin kamar yadda The Nation ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu
Wani mamba na cocin wanda ya tabbatar da sace faston ya ce wadanda suka sace shi sun taho ne cikin bakar mota kirar Toyota Corolla.
"A cikin coci aka sace shi. Sun zo da mota kirar Toyota Corolla mai launin baki. Shi kadai suka dauke," a cewarsa.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: FG Ta Sake Dawo da Dokar Kulle da Hana Taron Mutane Soboda Korona
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro ya tabbatar da sace faston yana mai cewa an fara bincike da nufin ganin an ceto shi sannan an kama wadanda suka sace shi.
Fasto Ogedengbe tsohon direkta ne a ma'aikatar ilimi na jihar Ondo.
A wani labarin daban kun ji cewa gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin ta tabbatar da cewa mutane shida sun mutu sakamakon wata bakuwar cuta a karamar hukumar Minjibir a jihar, Vangaurd ta ruwaito.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa wanda ya tabbatar da hakan ya ce wasu mutum 46 da suka kamu da cutar na jinya a asibiti.
Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla ne a kauyen Gandun Koya da ranar 7 ga watan Mayu kuma ta yadu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.
Asali: Legit.ng