'Yan Bindiga Sun kara Sace Limaman cocin Katolika Biyu A Kaduna

'Yan Bindiga Sun kara Sace Limaman cocin Katolika Biyu A Kaduna

  • Wasu ‘yan bindiga sun kara yi garkuwa da wasu limaman cocin Katolika guda biyu a jihar Kaduna
  • Anyi garkuwa da limaman cocin Katolika a lokacin da suke yin kiwo a ofishin cocin Christ The King Catholic Church, Yadin Garu
  • Shugaban cocin Katolika yayi kira da mabiya addinin Kirista dake yankin Kafanchan da su bi doka da Oda

Jihar Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu limaman cocin Katolika guda biyu a jihar Kaduna, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Rahotanni sun ce an yi garkuwa da limaman cocin guda biyu, Reverend Father John Cheitnum da Reverend Father Donatus Cleopas a yammacin ranar Juma’a a karamar hukumar Jere (LGA) ta jihar.

Sace su dai na zuwa ne kasa da mako biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wani limamin cocin Saint Charles Catholic Church, Zamina a karamar hukumar Kauru.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna A Jihar Filato

Kidnap
'Yan Bindiga Sun kara Sace Limaman cocin Katolika Biyu A Kaduna FOTO Daily Trust
Asali: Twitter

Ko da yake har yanzu hukumomin tsaro ba su tabbatar da faruwar lamarin ba, shugaban darikar Katolika na Kafanchan, Revrend Father Emmanuel Okolo, ya yi magana game da sace su da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Okolo ya ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da limaman cocin guda biyu da misalin karfe 5 na yammacin ranar Juma’a a lokacin da suke gudanar da aikin kiwo a ofishin cocin Christ The King Catholic Church, Yadin Garu.

Shugaban darikar Katolika ta yi addu’ar Allah ya dawo da limaman da aka sace cikin gaggawa sannan kuma ta bukaci mabiya darikar Katolika na Kafanchan da su ci gaba da bin doka da oda.

'Yan Bindiga Da yan ta'adan Ansaru sun fafata a jihar Kaduna

A wani labari kuma, Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ‘yan kungiyar ta’addar Ansaru hari a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna. Rahoton Daily Trust

Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan kungiyar suna yin wa’azi ga jama’ar yankin ne a lokacin da ‘yan bindiga suka bude wuta, inda suka kashe yan kauyen biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel