Yanzu yanzu : Abba kyari baya cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin kuje

Yanzu yanzu : Abba kyari baya cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin kuje

  • Hukumar gidan kaso na Najeriya ta ce dakataccen mataimakin kwamishinan dansanda Abba Kyari ya na nan bai tsere ba
  • Anyi nasarar kama fursunoni dari daga cikin fursunoni da suka tsere daga gidan kason kuje A Abuja
  • NCoS ta ce yan ta'adan da ake zargi mayakan kungiyar Boko Haram ne sunyi yunkurin shiga dakin da aka tsare Abba Kyari

Abuja - Rahoton da ya fito na cewa dakataccen mataimakin kwamshinan yansanda, Abba Kyari ya gudu daga gidan kaso na Kuje a daren ranar Talata karya ne kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Wani babban jami’in hukumar kula da gidan yarin Najeriya, NCoS, da ya zanta da wakilan jaridar Vanguard, yace yan ta’addan da suka yi amfani da bama-bamai dan samun shiga cikin gidan yari sun yi yunkurin shiga dakin da Abba Kyari ke tsare amma basu samu nasarar yin haka ba.

Kara karanta wannan

Harin gidan yarin Kuje: Atiku ya yi martani, ya bayyana babban damuwarsa kan lamarin

Hukumar Kula da Gidan Yari ta Najeriya (NCoS), a ranar Laraba, ta ce zaman lafiya ya dawo a gidan kaso dake Kuje bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai gidan kason.

KYARI
Yanzu yanzu : Abba kyari baya cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin kuje FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

Harin Yan bindigan da ake zargi mayakan Boko Haram ne suka kai gidan yarin, yayi sanadiyar tserewar fursununi dari shida wanda a ciki ake ta yamadidin cewa Abba Kyari, da tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye suna daga cikin fursunonin da suka gudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar NCos ta samu nasarar kama fursonuni dari daga cikin wadanda suka gudu bayan harin yan ta’ada.

Kamafanin simintin dangote ta bayyana shirin yadda zata samar da attajirai 25 a kowani wata

Jihar Legas- Kamafanin Simitin Dangote ta ce akalla mutane ashirin da biyar za su iya zama miloniya a cikin wata daya a wata gasar talla da ta ware Naira biliyan daya N1b mai taken “Spell Dangote and become a multi-millionaire.” Rahoton Jaridar PUNCH

Tallan wanda aka kaddamar a jihar Legas A ranar Talata tare da halartar jami’an hukumar kula da gasar da Caca na Najeriya NERC ana sa ran za ta bayar da kyaututtukan da za su canza rayuwan kwastomomin da za su yi wannan gasar ta hanyar siyan simintin kamfanin kamar yadda jaridar NewsNgr.com ta rawaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel