Da Dumi-Dumi: Hadimin Sheikh Gumi ya bayyana ƙungiyar da ta kai hari Kuje

Da Dumi-Dumi: Hadimin Sheikh Gumi ya bayyana ƙungiyar da ta kai hari Kuje

  • Tukur Mamu, hadimin Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ƙungiyar Ansaru ce ta kai hari gidan Yarin Kuje da ke birnin tarayya Abuja
  • Ya ce kungiya ɗaya ce da wadda ta kai hari kan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna a watan Maris
  • A cewarsa da ya sanar da hukumomin tsaro bayanan sirri na harin, amma yana zargin ba su ɗauki mataki

Abuja - Yan ta'addan Ƙungiyar Ansaru, waɗan da suka kai farmaki tare da sace Fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga watan Maris, su suka sake kai kazamin hari gidan Yarin Kuje ranar Talata da daddare.

Mai taimaka wa shahararren malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi, kan harkokin yaɗa labari, Malam Tukur Mamu, shi ne ya bayyana haka a Kaduna ranar Laraba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Harin Kuje: Kun Bani Kunya, Buhari Ya Fada Wa Hukumomin Tattara Bayanan Sirri

Gidan yarin da aka kai hari.
Da Dumi-Dumi: Hadimin Sheikh Gumi ya bayyana ƙungiyar da ta kai hari Kuje Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Mamu ya ce tun kafin 'yan ta'addan su kai harin, ya gaya wa hukumomin da abun ya shafa bayanan sirrin da ya samu amma yana zargin sun gaza ɗaukar mataki.

A wata sanarw ada ya fitar game da barazanar yanka fasinjoji da yan ta'adda suka yi da harin Kuje, Mamu ya jaddada cewa ya kai bayanan sirri ga hukumomin tsaro da kwamiti wanda shugaban dakarun tsaro, Janar Lucjy Irabor, ya kafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, ba bu tantama yan ta'adɗan da suka kai hari kan jirgin kasan Abuja-Kaduna, su ne suka ƙaddamar da mummunan hari a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Leadership ta rahoto Ya ce:

"Kuma duk da alamun da na gani na yunkurin kai hari wurare masu jan hankali kamar gidan Yarin Kuje, na garzaya na gaya wa hukumomin tsaro da wani kwamiti da CDS Lucky Urabor."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ɗan takarar shugaban kasa a 2023 ya buƙaci shugaba Buhari ya yi murabus

"Na tabbatar ba tare da tantama ba cewa ƙungiya ɗaya ce ta shirya ta kaddamar da harin gidan Yarin Kuje da kuma harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna saboda suna ba da alamu gab da kai harin wanda shi ne na sanar."

Da na cire hannu na amma an bani haƙuri - Mamu

Game da Fasinjojin da ke hannun yan ta'adda, Mamu ya ce bayan ya jagoranci kubutar da mutum 11 cikin 61 da ke tsare, ya yanke shawarin zare hannunsa kan lamarin saboda rashin damuwar gwamnati.

"Shugaba na, Sheikh Ahmad Gumi, ya ankarar da ni cewa saboda tausayin mutane na yi hakuri na cigaba. Amma ina tsammanin wannan ne na ƙarshe da zan tsoma kaina kan lamarin."

A wani labarin kuma Mayaƙan ISWAP da suka yi yunkurin kai kazamin hari Monguno da motocin yaƙi sun kwashi kashin su a hannun Sojoji

Sojojin haɗin guiwa na kasa da ƙasa MNJTF na runduna ta uku sun yi nasarar daƙile mummunan harin mayaƙan ISWAP a Borno.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo, ya dira gidan yarin Kuje

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce an kwashe fiye da a wa ɗaya ana ɗauki ba daɗi da yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel