Kicibis: NECO ta sa jarrabawa a ranar Sallah, Kungiya ta ce Musulmai za su je filin idi

Kicibis: NECO ta sa jarrabawa a ranar Sallah, Kungiya ta ce Musulmai za su je filin idi

  • Muslim Rights Concern ta ce an samu kicibis cikin jadawalin jarrabawar SSCE na shekarar bana
  • Idan aka tafi a haka, dalibai za su rubuta jarrabawa a lokacin da Musulmai ke bikin babbar sallah
  • Shugaban MURIC, Ishaq Akintola ya yi wa hukumar uzuri, ya ce ba da gan-gan aka samu cin karo ba

Nigeria - Kungiyar Muslim Rights Concern (MURIC) ta gabatar da roko na musamman ga hukumar NECO a game da jarrabawar da ake yi a yanzu.

Daily Trust ta ce shugaban kungiyar MURIC na kasa, Farfesa Ishaq Akintola ya roki NECO ta canza jadawalin jarrabawar na ta saboda an samu kicibis.

Hukumar NECO ta sa jarrabawa a ranar 9 ga watan Yulin 2022, a wannan ranar ne kusan duka musulman da ke fadin Duniya za su yi bikin babbar sallah.

Kara karanta wannan

INEC ta bayyana damuwarta akan karancin rajistar katin zabe a jihar Katsina

Farfesa Ishaq Akintola yake cewa a daidai safiyar ranar Asabar mai zuwa da Musulmai ke shirin zuwa filin idi, NECO ta tsara za a rubuta wata jarrabawar.

“NECO ta sa wata jarrabawarta, Data Processing (Practical) a ranar 9 ga watan Yuli daga karfe 10:00 na safe zuwa 1:00 na yamma.”
“Sai dai kuma an samu kicibis, wannan rana ta ci karo da ranar farko na bikin babbar sallah.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarrabawar SSCE
Dalibai Masu jarrabawa Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

“A duba jadawalin jarrabawar NECO na 2022 (Babbar jarrabawar SSCE ta 2022 NECO na Yuni/Yuli (27 ga Yuni – 12 ga Agustan 2022)

- Farfesa Ishaq Akintola

MURIC ta ba NECO uzuri

“Mu na sane da cewa ba da gan-gan NECO ta hada wannan karo ba, domin NECO kan nuna karamci, ta ware tsawo mako guda na murnar sallah.

- Farfesa Ishaq Akintola

Farfesa Akintola yake cewa daga ranar Litinin, 11 ga watan Yuli, har zuwa Juma’a watau 15 ga wata, ba za a rubuta wata jarrabawa ba saboda bikin sallah.

Kara karanta wannan

A Zurfafa Bincike Kan Yaran Musulmi 21 Da Aka Ceto a Cocin ECWA Plateau, In Ji MURIC

Kungiyar Musulman ta ce wannan ya nuna tun farko hukumar jarrabawar ta san da zaman idi, a dalilin haka, da gan-gan ba za ta sa wa dalibai jarrabawa ba.

A kai jarrabawar zuwa Alhamis

“Don haka mu na kira ga jami’an NECO da su canza lokacin jarrabawar nan ta Asabar, zuwa wata ranar dabam domin Musulmai su rubuta jarrabawar.”
“Takardar da aka tsara za a rubuta a ranar sallah, za ta iya komawa ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli 2022, wanda ta na cikin ranar hutun da aka bada.”
“MURIC ta na yi wa NECO da ma’aikatanta da jami’anta da ‘yan Najeriya barka da sallah."

- Farfesa Ishaq Akintola

Asali: Legit.ng

Online view pixel