Karancin rajistar katin zabe a jihar Katsina ya ta da hankalin INEC

Karancin rajistar katin zabe a jihar Katsina ya ta da hankalin INEC

  • Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Katsina ta bayyana damuwarta kan yadda ake samu karancin rijistar katin zabe
  • Kwamishinan INEC na jihar Katsina ya alakantar da karancin yin rajista da matsalar harkar tsaro da jihar ke fuskanata
  • Zarewa ya ce kananan hukumomi 17 a jihar sunyi watanni biyar da yanke musu kafofin sadarwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina : Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Katsina ta bayyana damuwarta kan yadda al,ummar jihar basa yin rijistar katin zabe na dindindin a sabbin rumfunan zabe 1,750 da aka kafa a jihar.

Kwamishina INEC na jihar, Alhaji Jibril Zarewa, ya bayyana haka a lokacin da ya zanatawa da manema labaran News Agency of Nigeria a ranar Juma’a kamar yadda PUNCH ta rawaito

Ya ce shakara daya kenan bayan kaddamar da sabbin rumfuna rajistar katin zabe amma mutane da dama basu fito yin rajista ba.

Kara karanta wannan

Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman

Legit NG
Karancin rajistar katin zabe a jihar Katsina ya ta da hankalin INEC
Asali: Depositphotos

Zarewa yace ,

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Bisa bincikin da suka yi a watan Mayu 2022 cikin rumfuna 1,750 da suka kaddamar, rumfuna 1,200 basu samu sama da mutane 50 da sukayi rajista a kowani rumfa ba.
“Duk da yake an samu matsalar yanke kafofin sadarwa a kananan hukumumi 17 daga cikin 34 na jihar na watanni biyar saboda matsalar harkar tsaro," Inji shi.

Ta tabbata: INEC ta amince da takarar gwamnan Kano ga dan janar Abacha a PDP

A wani labari - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tabbatar da cewa ta sa idon basira a zaben fidda gwani da ya samar da Mohammad Abacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Kafin bayanin na INEC dai an yi ta cece-kuce kan wanda hukumar za ta amince da shi a matsayin dan takarar gwamna tsakanin Mohammed Abacha da Sadiq Wali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel