Hedkwatar tsaro: 'Yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 4,770 sun mika wuya cikin makwanni 2

Hedkwatar tsaro: 'Yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 4,770 sun mika wuya cikin makwanni 2

  • Rundunan sojin Najeriya ta sanar da irin ayyukan da jami'anta suka yi a cikin kwanakin nan a yankunan kasar nan
  • A cewar rundunar, akalla 'yan ta'addan Boko Haram 4770 ne suka mika wuya a cikin kasa da makwanni biyu
  • Hakazalika, rundunar ta ce, ta kama wasu tsageru tare da kwato wasu kayayyaki da mutanen da aka sace

Abuja - Hedikwatar tsaro ta ce ‘yan ta’adda 4,770 da suka kunshi manya maza 864 da mata 1,415 da kananan yara 2,490 ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya tsakanin ranakun 1 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yuni a yankin Arewa maso Gabas.

Daraktan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Bernard Onyeuko, ya bayyana haka ne a taron manema labarai na mako-mako kan ayyukan rundunar a ranar Alhamis, a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

'Yan ta'adda da dama sun mika wuya
Hedkwatar tsaro: 'Yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 4,770 sun mika wuya cikin makwanni 2 | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Onyeuko ya ce sojojin Operation Hadin Kai sun kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu a wurare daban-daban na shiyyar Arewa maso Gabas.

Ya ce ayyukan sun kai ga ceto mutanen da aka sace, da kawar da ‘yan ta’adda da dama, kame ‘yan ta’addan, kwato makamai da alburusai da sauran abubuwan da suka shafi tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onyeuko ya ce sojojin bataliya ta 152 a tsakanin 17 ga watan Yuni zuwa 21 ga watan Yuni sun yi arangama da mayakan Boko Haram da ke tserewa a Buduwa da ke karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Ya kara da cewa an kwato shanu 14 da aka sace da kuma kekuna uku tare da kama wasu masu hada kai da ‘yan ta’adda da kuma masu samar musu da kayayyakin aiki.

An kama kasurguman 'yan Boko Haram

A cewarsa, an kama Malam Abacha Usman a Benshek, Malam Ibrahim Gira da ke kan titin Damboa – Biu da kuma Malam Ibrahim Gira – wani mai samar da man fetur ga tsagerun.

Kara karanta wannan

Borno: Bidiyo ya nuna lokacin da 'yan Boko Haram 314 ke mika wuya ga jami'an sojoji

Ya ce, sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 11, sun kama 11 tare da kwato shanu 14, bindigogi kirar AK47 guda biyu, kekuna uku, bindigogin gida guda biyu, harsasai 90 masu girman 7.62mm, da mota kirar Golf 2 guda daya.

A cewarsa:

"An dauki bayanan dukkan 'yan ta'addar Boko Haram/Islamic State West Africa Province da iyalansu da suka mika kansu yayin da aka mika su ga hukumar da ta dace domin daukar mataki."

Hakazalika, ya yi bayanai game da sauran ayyukan rundunar sojin kamar yadda jaridar Daily Sun ta ruwaito.

Bidiyo ya nuna lokacin da 'yan Boko Haram 314 ke mika wuya ga jami'an sojoji

A wani labarin, a yau 29 ga watan Yuni ne rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar karbar akalla 'yan ta'addan Boko Haram 314 da suka mika wuya a karamar hukumar Bamata jihar Borno.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jami'an soji ke ci gaba da matsa lamba ga kakkabe 'yan ta'aadda a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Alkali ya yanke hukunci a kan Budurwar da tayi karyar an sace ta

A wata sanarwar da rundunar sojin ta fitar mai dauke da hotuna da bidiyo, an ga lokacin da jami'an ke karbar 'yan ta'addan cikin adadi mai yawa, tare da kokarin tantance su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel