‘Yan Majalisa sun tono wanda Shugaban kasa ya ba mukami bai da shaidar karatun Firamare

‘Yan Majalisa sun tono wanda Shugaban kasa ya ba mukami bai da shaidar karatun Firamare

  • Joe Anekhu Ohiani ya bayyana a gaban majalisa domin a tabbatar da shi a matsayin shugaban ICRC
  • Kwamitin Muhammad Adamu Aliero ya fahimci ashe Joe Anekhu Ohiani bai da takardar gama firamare
  • Shugaban ICRC na rikon kwarya ya fadawa ‘Yan majalisa cewa ya tafi sakandare ne daga aji biyar

Abuja - A ranar Laraba, 29 ga watan Yuni 2022, Majalisar dattawa ta gano cewa wanda ake so ya zama shugaban hukumar ICRC ta kasa yana da nakasa.

Rahoton da ya fito daga Vanguard ya tabbatar da cewa Joe Anekhu Ohiani bai da takardar kammala firamare domin bai karasa karatu ba, ya yi gaba.

Mista Joe Anekhu Ohiani ya tsaida karatun firamarensa ne a aji biyar, don haka bai da satifiket.

Kamar yadda ya fada da bakinsa Ohiani ya ce a aji biyar ya rubuta jarrabawar shiga sakandare, ya samu nasara, uzurin da Sanatocin sam ba su karba ba.

Kara karanta wannan

Wani shahararren gwamnan PDP: Har yanzu Allah bai yarje min na goyi bayan Atiku ba

A dalilin haka Sanatoci suka bukaci ya gabatar da wata hujja da za ta nuna cewa lallai ya yi makarantar firamare kamar yadda doka tayi tanadi.

Kwamitin Sanata Aliero

Mista Joe Ohiani wanda ya fito daga garin Ohaini a karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi ya bayyana ne a gaban kwamitin Muhammad Adamu Aliero.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

‘Yan Majalisa
Zauren Majalisar Dattawa Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Sanata Muhammad Adamu Aliero shi ne shugaban kwamitin ayyuka a majalisar dattawa, don haka kwamitinsa zai tantance wanda zai rike hukumar ICRC.

Rahoton ya ce Sanatocin sun gamsu da sauran takardun da Ohiani ya gabatar, amma suka ce akwai bukatar ya nuna lallai ya yi karatu a makarantar firamare.

A halin yanzu John Ohiani ya na rike da ICRC ne a matsayin shugaban rikon kwarya, ba a tantance shi ba, yana cikin wadanda aka fara aiki da su a 2009.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa APC ta hana ni damar komawa Majalisa – Sanata ya fayyace komai

Ohiani ya yi karatu a Jami'a

Wanda ake so ya zama shugaban na ICRC kwararren Lauya ne wanda ya yi karatu a jami’ar ABU Zaria, kuma ya yi aiki a wasu kwamitoci na shugaban kasa.

Ohiani ya amsa tambayoyin kwamitin majalisar dattawan har Sanata Aliero ya ce akwai bukatar ya zo da dabarun da za su sa gwamnati ta rage yawan cin bashi.

Kabiru Masari bai ba INEC takardu ba

Ku na da labari shi ma ‘dan takarar wucin gadi na APC, Alhaji Kabiru Ibrahim Masari ya tabbatar da cewa takardun shaidar duk karatun da ya yi a baya sun bace.

Masari ya sanar da ‘yan sanda game da bacewar, ya rubuta takardar rantsuwa domin ya wanke kansa. Wannan takarda ya ba INEC a madadin satifiket din sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel