Abin da ya sa APC ta hana ni damar komawa Majalisa – Sanata ya fayyace komai

Abin da ya sa APC ta hana ni damar komawa Majalisa – Sanata ya fayyace komai

  • Mohammed Adamu Bulkachuwa ya koka a kan yadda abubuwa suka faru da APC a jihar Bauchi
  • Sanata Bulkachuwa yake cewa ba a bi shawarar da ya bada ba, hakan ta sa Sanatoci 2 su ka bar APC
  • ‘Dan majalisar ya ce sai da ya yi magana da Adamu Adamu, amma Ministan ya ki daukar shawara

Abuja - Mohammed Adamu Bulkachuwa mai wakiltar Arewacin jihar Bauchi a majalisar dattawa, ya yi karin haske kan rasa tikitin zaben 2023 da ya yi.

Sanata Mohammed Adamu Bulkachuwa ya bayyana wannan da aka yi wata hira ta musamman da shi a gidan talabijin nan na Channels TV a ranar Talata.

Mohammed Adamu Bulkachuwa ya bayyana cewa ana ta samun wasu matsaloli a APC, don haka shi ya zabi ya zame hannunsa daga zaben fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Takardun makarantar da Atiku, Tinubu, Kwankwaso da Obi suka gabatarwa hukumar INEC

A lokacin da shugabannin jam’iyyar APC na kasa suka turo kwamitin da zai gudanar da zaben tsaida ‘yan takara a Bauchi, Bulkachuwa ya kai korafinsa.

Kwamitin tsaida 'yan takara a Bauchi

“Kowa yana da hanyar da yake nuna fushinsa. Abin da ya sa na fita daga takarar abu ne mai matukar sauki.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Na kai kuka gaban wadanda aka aiko daga Abuja domin su shirya zaben ‘yan takarar Gwamna da na Sanatoci.”
“Na yi magana da su, amma bisa dukkan alamu sun zo garin Bauchi ne da wata niyya a dunkule a cikin zuciyarsu.”
Sanatoci
Zaman Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

Na yi magana da Adamu Adamu

Kamar yadda Sanatan ya shaidawa gidan talabijin, ya yi kokarin gamsar da kwamitin zaben, amma ba a samu fahimtar juna tsakaninsa da ‘yan jam’iyyar ba.

An rahoto Mai gidan tsohuwar shugaban kotun daukaka karar kasar yana mai cewa ya tattauna da Adamu Adamu domin ganin yadda APC za ta iya lashe zabe.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

“Jagorori da wanda aka ba nauyin shugabantar APC a Bauchi, Ministan ilmi, Adamu Adamu da ni mun tattauna, na ba shi shawarar yadda za a tsira.”
“Na fadi yadda abubuwa za su tafi kalau, ba tare da APC tayi asara ba. Tun da ba ayi amfani da shawarar ba, biyu daga cikin abokan aikina sun tsere.”

NNPP ta samu Sanatoci a Bauchi

Kwanakin baya kun ji labari cewa Sanatan kudancin jihar Bauchi, Lawan Yahaya Gumau ya tattara kayan shi, ya hakura da APC bayan an hana shi shiga takara.

Sannan kun ji Sanata Halliru Dauda Jika ya fice daga APC bayan shan kashi a zaben zama ‘dan takarar Gwamna, ya koma NNPP inda ake tunanin shi za a ba tikiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel