Korar Ma’aikata 30,000 da El-Rufai Ya Yi Ne Ya Janyo Matsalar Tsaro a Kaduna, Ƙungiyar Ƙwadago

Korar Ma’aikata 30,000 da El-Rufai Ya Yi Ne Ya Janyo Matsalar Tsaro a Kaduna, Ƙungiyar Ƙwadago

- Kungiyar kwadago ta alakanta karuwar rashin tsaro a jihar Kaduna ta korar ma'aikata a jihar

- Kungiyar ta bayyana haka ne yayin bikin ranar ma'aikata yau a babban birnin tarayya Abuja

- Kungiyar ta ce bata goyon bayan gwamnatin Kaduna akan matakin korar karin ma'aikata 5,000

Kungiyar kwadago na kasa reshen jihar Kaduna ta alakanta rashin tsaro a jihar da korar ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi, The Nation ta ruwaito.

Kungiyar ta ce gwamnatin Nasiru El-Rufai ta kori ma'aikata 30,000 tun bayan hawa karagar mulki a shekarar 2015.

Korar Ma’aikata 30,000 da El-Rufai Ya Yi Ne Ya Janyo Matsalar Tsaro a Kaduna, Ƙungiyar Ƙwadago
Korar Ma’aikata 30,000 da El-Rufai Ya Yi Ne Ya Janyo Matsalar Tsaro a Kaduna, Ƙungiyar Ƙwadago. Hoto: @dail_trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An Harbe Auwalu Daudawa Har Lahira Kwana Huɗu Bayan Komawarsa Daji

Babban sakataren kungiyar hadaka ta AUPCTRE, Comrade Sikiru Waheed, shi ne ya bayyana haka yayin bikin ranar ma'aikata a Abuja.

AUPCTRE, reshen kungiyar gwadago ta kasa, ta ce za ta goyi bayan kungiyar kwadago kan makomar ma'aikatan a Kaduna.

Kungiyar kwadago tayi barazanar dakatar da al'amura a jihar Kaduna biyo bayan yunkurin gwamnati na korar ma'aikata 5,000.

KU KARANTA: Jerry Gana Ya Yi Barazanar Maka Majalisar Ƙolin Musuluncin Nigeria a Kotu

Ya ce, "AUPCTRE na amfani da ranar ma'aikata ta 2021 don tabbatarwa ma'aikata da shugabannin su, karkashin jagorancin Comrade Ayuba Wabba cewa suna tare da kungiyoyin ma'aikata bisa nuna rashin goyon baya kan matakin da gwamna El - Rufai na korar karin ma'aikata 5,000 a watan da ya wuce, wanda hakan ya kai kusan korar ma'aikata 30,000 daga 2015 zuwa yau.

"Wannan na daga cikin dalilan karuwar rashin tsaro a Jihar Kaduna da makwabtan jihohi kamar Niger, Abuja da Kogi."

Kungiyar ta yabawa ma'aikata da jajircewar su duk da kalubalen da annobar COVID - 19 ta haddasa.

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164