Sarki da Hakimi sun rasa kujerunsu a dalilin mummunar rigimar da ta barke a kan fili

Sarki da Hakimi sun rasa kujerunsu a dalilin mummunar rigimar da ta barke a kan fili

  • Ana ta faman rikici a kan filaye a yankin Nko a garin Obol Etim Ayomobi da ke cikin Kuros Riba
  • Wannan rigima da ake yi a jihar ta yi sanadiyyar mutuwar Bayin Allah da asarar dinbin dukiya
  • Hakan ta sa Gwamna Ben Ayade ya tsige sarakunan, ya nemi sojoji su gano masu tada kayar baya

Cross River - Gwamnatin jihar Kuros Riba ta bada umarnin a tunbuke Mai martaba Obol Lopon na kasar Nko, a garin Obol Etim Ayomobi da ke yankin Yakurr.

Rahoton da mu ka samu a ranar Talata, 28 ga watan Yuni 2022 daga Punch ya tabbatar da cewa Obol Lopon ya rasa sarautarsa a karamar hukumar Obubra.

Haka zalika Gwamnatin jihar Ribas ta tsige Hakimin Onyadama watau Mai martaba Ovarr Vincent Erena. Matakin zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Kuma dai: Yan bindiga sun sake sace wani limamin Katolika a jihar Edo

Jaridar ta ce masu sarautar sun rasa mukamansu ne a dalilin rikicin da ya barke tsakanin kauyakan Nko, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayuka.

Baya ga rasa rayuka, gwamnatin jihar Kuros Riba ta ce mutane sun yi asarar dukiya a garin Obubra.

Gwamna ya sauke Sarakuna

Wani jawabi da ya fito daga Babban Sakataren yada labaran gwamna Ben Ayade watau Linus Obogo, ya fitar da jawabin tsige wadannan masu sarauta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Osinbajo a Kalaba
Sarakunan Kuros Riba a gidan Gwamnati Hoto: theparadise.ng
Asali: UGC

Linus Obogo ya ce tunbuke wadannan masu sarauta biyu da duk wasu masu sarautar gargajiya a yankin ya zo ne dalilin kashe-kashen da mutane su ka rika yi.

Rikicin fili da ake yi

Mutanen Nko da na Onyadama sun dade su na rigima kan fili, hakan ta sa gwamnatin Ben Ayade ta karbe wannan fili da ya jawo rigima, domin a zauna lafiya.

Kara karanta wannan

Gaskiyar abinda Sanata Ekweremadu da matarsa suka faɗa wa Kotun Landan kan zargin yanke sassan jiki

Bayan karbe filin, gwamna Ben Ayade ya bada umarni ga sojoji da baza wuta a yankin Nko, har sai an kama mutanen da ake zargi da laifin kashe wasu sojoji.

Jami’an sojoji shida aka hallaka a garin Nko a wajen wannan mummunan rikici da ya barke.

Rahoton ya ce tuni jagoran APC na kasa, Cif Okoi Obono Obla, wanda daga wannan yanki ya fito, ya fitar da jawabin yana Allah-wadai da abin da ya wakana.

Kuros Riba ta APC ce

Ku na da labari cewa duk mutanen jihar Kuros Riba za su dangwalawa APC a zaben 2023. Ben Ayade ne ya yi alkawarin kawowa Bola Tinubu kuri'unsa.

A baya Gwamna David Umahi ya yi irin wannan alkawarin, ya ce APC za ta ci zabe a jihar Ebonyi, ya ce babu wanda zai zabi Peter Obi da Jam’iyyarsa ta LP ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel