Kuma dai: Yan bindiga sun sake sace wani limamin Katolika a jihar Edo

Kuma dai: Yan bindiga sun sake sace wani limamin Katolika a jihar Edo

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da wani limamin Katolika, Rev Fr. Osia a garin Ikabigbo da ke karamar hukumar Etsako ta yamma na jihar Edo
  • Maharan sun farmaki malamin addinin ne a gidansa yayin da yake shirin zuwa taron addu'a a yau Lahadi, 26 ga watan Yuni
  • Basaraken garin, Bramah Alegeh, wanda ya tabbatar da lamarin, yace ana kokarin ganin an ceto malamin

Edo - Yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin Katolika mai suna Rev Fr. Christopher Odia a garin Ikabigbo da ke karamar hukumar Etsako ta yamma na jihar Edo a safiyar ranar Lahadi, 25 ga watan Yuni, jaridar The Sun ta rahoto.

An tattaro cewa malamin addinin na shirin zuwa taron addu’a na ranar Lahadi lokacin da yan bindiga suka farmaki gidansa sannan suka yi awon gaba da shi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari birnin Katsina, sun yi garkuwa da mazauna yankin da dama

Rev. Father Osia
Kuma dai: Yan bindiga sun sake sace wani limamin Katolika a jihar Edo Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wata majiya a garin ta sanar da Daily Trust cewa tuni kungiyar yan bangar garin suka kakkabe jeji don ceto malamin.

Ya ce yan bindigar sun harbi daya daga cikin matasan garin da ke neman malamin, inda ya kara da cewa an kwashi matashin zuwa wani asibiti a Auchi amma aka mayar da su asibitin kwararru na Irrua don ganin likita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sarkin garin, Bramah Alegeh, wanda ya tabbatar da lamarin, yace ana kokarin ganin an saki malamin.

Ya ce yan sanda da sojoji da taimakon yan banga suna bincikar jejin don tabbatar da sakinsa.

Da aka tuntube shi, Kakakin yan sandan jihar Edo, SP Chidi Nwanbor, ya ce zai kira baya.

Yan bindiga sun kashe wani malamin addini a jihar Kaduna

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wasu yan bindiga sun kashe babban malamin darikar Katolika na kwalejin fasaha ta jihar Kaduna, Rev. Fr. Vitus Borogo a ranar Asabar, 25 ga watan Yuni, a gonarsa da ke hanyar Kaduna-Kachia.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun fille kan wani tsohon dan majalisa

Shugaban darikar Katolika a jihar Kaduna, Rev. Fr. Christian Emmanuel, ya tabbatar da faruwa lamarin a wata sanarwa da aka gabatarwa kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kaduna.

Emmanuel ya ce an kashe Marigayi Borogo a gonar gidan yari, Kujama, hanyar Kaduna zuwa Kachia, bayan wasu da ake zaton yan ta’adda ne sun farmaki gonar, jaridar The Guardian ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel