Yanke sassan jikin mutum: Abinda Sanata Ekweremadu da matarsa suka faɗa wa Kotu a Landan

Yanke sassan jikin mutum: Abinda Sanata Ekweremadu da matarsa suka faɗa wa Kotu a Landan

  • Sanata Ike Ekweremadu da matarsa sun gurfana a gaban Kotun Majirstire a Landan, kuma sun yi kokarin kare kan su kan zargin safara
  • Ta bakin lauyoyin su, Gavin Irwin da Antonia Gray, sun musanta tuhumar da ake musu na safarar mutane da nufin yanke sassan jikin su
  • Yan sandan Landan, babban birnin ƙasar Birtaniya sun kame ma'auratan ne da zargin safarar wani yaro da niyyar amfani da sassan jikinsa

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, da mai ɗakinsa Beatrice, sun musanta zargin da 'yan sandan Landan suke musu na safarar mutane a zaman Kotun Birtaniya.

A wani rahoto da Daily Mail ta tattara, lauyoyin sanatan da matarsa, Gavin Irwin da Antonia Gray ne suka yi jawabi a madadin waɗan da ake zargi da nufin su samar musu beli.

Kara karanta wannan

Ekweremadu na hanyar zuwa Turkiyya sayan sabuwar koda muka kwamushe shi, Lauyoyi

Sanata Ike Ekweremadu da matarsa.
Yanke sassan jikin mutum: Abinda Sanata Ekweremadu da matarsa suka faɗa wa Kotu a Landan Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Rahoton wanda aka yi yayinsa sosai a kafafen sada zuminta, an masa taken, "Abin da lauyoyin Sanata Ekweremadu suka faɗa."

A ruwayar The Nation, rahoton ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A bayanan da Mista Ekweremadu ya shirya ya musanta zargin safarar mutane ya ce babu inda ya shirya safarar ko mutum ɗaya da nufin yanke sassan jikinsa. Haka matarsa, a bayaninta ta musanta zargin a zaman Kotu."
"Lauyan da ya wakilci Sanatan, Gavin Irwin ya ce: Babu tambaya wannan babbar tuhuma ce, Ekweremadu mamba ne a majalisar dattawan Najeriya. A baya ya rike babban muƙami na mataimakin shugaban majalisa."
"Mamba ne a ƙungiyar lauyoyi a Najeriya, babban masanin doka ne. Idan muka tattara waɗan nan abubuwan ya zarce zama mai kyaun hali sai dai shi mutum ne da ya jagoranci kamilallun mutane. Tuhumar da ake masa ta saɓa wa hankali."

Kara karanta wannan

Safarar Sassan Jikin Mutum: Za A Iya Yi Wa Ekweremadu Da Matarsa Daurin Rai Da Rai A Birtaniya

A ɗaya ɓangaren kuma, Antonia Gray, a madadin matar Ekweremadu, ya ce:

"Ba ta taɓa shiga rikici ba ko aka gano hannun ta a wani zargin safarar ƙananan yara ba bisa ƙa'ida ba a tarihi. Ta kasance Akantar kuɗi da ta yi aiki mai kyau."

A wani labarin kuma Sanata Ekweremadu da matarsa sun shiga tsaka mai wuya domin za'a iya yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai idan aka kama su da laifi

Dokar Birtaniya ta Modern Slavery Act, 2015 (MSA 2015) ta tanadi laifi mai tsauri da ya kama daga daurin watanni 12 a gidan gyaran hali har zuwa daurin rai da rai a gidan gyaran hali.

An gurfanar da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawar na Najeriya da matarsa a kotu a ranar Alhamisa a Birtaniya kuma ba a belinsu ba bayan kotun ta fara sauraron karar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel