Ta'addanci: Sojoji sun kakkabe mafakar IPOB/ESN, sun kwato makamai masu hadari

Ta'addanci: Sojoji sun kakkabe mafakar IPOB/ESN, sun kwato makamai masu hadari

  • Rundunonin tsaron Najeriya da ke yaki da 'yan ta'addan IPOB da ESN sun yi nasarar fatattakar mafakar tsageru
  • Wannan na zuwa a karshen mako, daidai lokacin da jami'an suka kai samame jihohin Anambra da Enugu na yankin
  • A wata sanarwa, an bayyana irin kayayyakin da aka kwato daga hannun tsagerun da kuma kokarin da jami'ai suka yi

Kudu maso Gabas - Rundunonin tsaron Najeriya sun yi nasarar fatattakar mafakar 'yan ta'addan IPOB a jihar Anambra ta yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Wata sanarwa da tsohon mukaddan soji SK Usman ya yada, sanye da hannun Brig. Gen. Onyema Nwachuku ta bayyana irin arangamar da jami'an na sojin kasa, sama, DSS, 'yan sanda da sauransu suka yi, lamarin da ya kai kwato masu muggan makamai masu hadarin gaske.

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

An fatattaki 'yan IPOB, an kwato makamai
Ta'addanci: Sojoji sun kakkabe mafakar IPOB/ESN, sun kwato makamai masu hadarin gaske | Hoto@ SK Usman
Asali: Facebook

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami'ai sun yi amfani da nakiya wajen fito da tsagerun daga mafakarsu, kuma an yi nasarar kassara karfinsu a sansanin.

A cewar wani bangare na sanarwar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa da ta kunshi sojojin runduna ta 302 na sojojin Najeriya, da jami’an sojin ruwa na Najeriya, da jami'an farin kaya da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya sun tarwatsa sansanonin ‘yan IPOB da kuma ESN a Idara, kauyukan Nnebo, Ihe Mbosi da Ukpor dake karamar hukumar Nnewi ta kudu a jihar Anambra.
"A wani aikin share fage da aka gudanar da sanyin safiyar ranar Asabar 25 ga watan Yunin 2022, sojojin sun fatattaki ‘yan kungiyar ta IPOB da na’urori masu fashewa don korar 'yan ta'addan daga maboyarsu.
"A yayin samamen, sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, mujallu uku dauke da harsashi biyar na 7.62 mm (na musamman), bindigogin famfo guda biyu da kuma bindigar gida guda daya. Sauran abubuwan sun hada da janareta guda uku, da sauransu."

Kara karanta wannan

Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

A bangare guda, wani samamen a jihar Enugu ya kai ga fatattakar tsagerun tare da kwato makamai masu hadari da kuma motocin da ake zargin na sata ne.

An fatattaku 'yan IPOB a Enugu

Sanarwar ta ce:

"Hakazalika, sojojin bataliya ta 103 sun kai wani samame a sansanin IPOB/ ESN dake dajin Nkwere Inyi a karamar hukumar Oji ta jihar Enugu.
"Arangamar ta tilasta wa 'yan ta'addan tserewa cikin rudani, yayin da sojoji suka samu mota Lexus daya da Toyota Highlander SUV da ake zargin miyagun sun sato ne. Sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da babura biyu, bindiga biyu da kuma harsashi guda bakwai."

Karshe, sanarwar ta yi kira ga mazauna da su zama masu sanar da jami'an tsaro duk wani motsin 'yan ta'adda tare ba da rahotanni da hadin kai da zai kai ga wanzar da zaman lafiya.

Nasara: Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

Kara karanta wannan

Nasara: Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

A wani labarin, kafar labarai ta Channels ta ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan ta'adda shida a fagagen ayyukan ta daban-daban.

Mahukuntan sojojin sun kuma ce sojojin sun kama wasu da ke hada kai da maharan, ciki har da wani fitaccen dillalin bindigu da kuma samar da kayan aikin Boko Haram.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwa da kakakinta, Manjo Janar Bernard Onyeuko ya fitar, hedkwatar tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel