Hukumar Hisbah Za Ta Kafa Sharruda Kan Kafofin Sada Zumunta

Hukumar Hisbah Za Ta Kafa Sharruda Kan Kafofin Sada Zumunta

  • Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta na aiki domin saka sharruda kan amfani da shafukan sada zumunta irinsu Tik Tok, Instagram da sauransu
  • Hisbah ta ce ta kafa kwamiti tare da hadin gwiwa da hukumar tantance fina-finai na Jihar Kano don bullo da sharruda da za su hana aikata badala a shafukan
  • Ismail Na'abba Afakallah, shugaban hukumar tace fina-finai na Kano ya kuma shawarci iyaye su saka ido kan abin da yayansu ke yi a dandalin sada zumunta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano a halin yanzu tana shirin yin dokar kafa sharruda kan amfani da kafafen sada zumunta wato soshiyal midiya.

Domin hakan, hukumar tana hadin gwiwa da Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano (KSCB).

Jami'an Hisbah.
Hisbah Za Ta Kafa Sharruda Kan Kafofin Sada Zumunta. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Fulani Ba Yan Ta'adda Bane, In Ji Sheikh Ahmad Gumi

Ismail Na'abba Afakallah, Babban Direktan KSCB, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi, Daily Trust ta rahoto.

Dandalin sada zumuntar na lalata tarbiyar yaran mu, Afakallah

Ya ce hukumar ta sa za ta mayar da hankali ne sosai kan fim industry, soshiyal midiya, musamman TikTok, da ya bawa masu karfin fada a ji a dandalin sada zumunta aikata badala.

"Hukumar mu da Hisbah ta kafa kwamiti da zai samar da hanyoyin magance wannan matsalar. Ba jaruman Kannywood kadai ke aikata badala ba a Tik Tok, mafi yawancin masu badala da shi ba yan industry bane.
"Kallubale da ta shafi duniya. Mutane na ganinsa cewa duniya ce kuma za su iya duk abin da suke so. Kuma ba za mu iya barin hakan ya bata tarbiyar yaran mu ba.
"Mun damu da yan Tik Tok wadanda ba yan fim bane saboda suna bata tarbiyyar yaranmu. Ma za mu amince da rashin tarbiyya ba. Dandalin ta zama sanadin kashe aure, bata tarbiyya da wasu abubuwan."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An kwato tsabar N170m, motoci da sauran su daga hannun wani babba a Abuja

Ya bayyana damuwarsa kan cewa an kirkiri dandalin sada zumunta ne don nishadi da watsa bayanai masu amfani amma mutane suna amfani da shi ta hanyar da bai dace ba.

"Yanzu suna amfani da damar don yada bayanai marasa amfani. Za ka ga manyan mata suna tika rawa na rashin mutunci da wasu abubuwan rashin tarbiya, musamman a Tik Tok da Instagram."

Ya yi kira ga iyaye su saka idanu kan abin da yayansu ke yi a soshiyal midiya don kada su lalace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel