Da dumi-dumi: ICPC ta kwato N170m, motoci da wasu kayayyaki daga hannun dan kwangilar soja a Abuja

Da dumi-dumi: ICPC ta kwato N170m, motoci da wasu kayayyaki daga hannun dan kwangilar soja a Abuja

  • A babban birnin tarayya Abuja, jami'an hukumar ICPC sun yi babban kamun da ake zargin kayan rashawa ne
  • An ruwaito cewa, hukumar ta kama wasu kayayyaki ciki har da motoci da agogi masu matukar tsada ainun
  • A cewar hukumar ta ICPC an kama kayan ne a wani samame da jami'an hukumar suka kai kan wani gini

Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta kwato tsabar kudi Naira miliyan 170, dala $220,965, mota G-Wagon da sauran kayayyaki daga hannun wani dan kwangilar soja a Abuja.

Azuka Ogugua, kakakin hukumar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ogugua ya ce bisa ga bayanan sirri, hukumar ta kai samame a wani gida da ke Wuse 2, Abuja, inda aka gano kayayyakin masu tsada.

Kara karanta wannan

Kotu ta Bada Umarnin Kwace Kadarar Ɗan Sambo Dasuki Dake Abuja

Yadda ICPC suka kwamushe kayayyaki masu daraja
Yanzu-Yanzu: ICPC ta kwato tsabar kudi N170m, G-Wagon da sauran su daga hannun dan kwangilar soja a Abuja | Hoto: icpc.gov.ng
Asali: UGC

A cewar sanarwar:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“An jawo hankalin hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) kan wasu rahotannin da ba su da inganci kuma gurbatattu a kafafen yada labarai game da kama wasu kudade biliyoyin nairori, daloli, agogon Rolex da aka jibge a gini a Abuja.
“Hukumar tana so ta bayyana cewa jami’an ICPC sun kai samame kan wani gini a Wuse 2 na babban birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuni, 2022 tsakanin karfe 5:00 na yamma zuwa 12:00 na safe bisa zargin karkatar da kudade.
"Bayanan da ake da su a halin yanzu sun nuna cewa kadarorin mallakar mai kamfanin K Salam Construction Company ne, dan kwangilar soja.
“Hukumar ta kwato kudi da wasu kayayyaki daga cikin kadarorin kamar haka, N175,706,500; $220,965; G-Wagon; mota bugun 2022 na BMW da Mercedes Benz; wayoyin hannu na musamman; agogon hannu masu tsada, gami da Rolex uku, da wasu takaddun kadarorin."

Kara karanta wannan

Jami’an Sojoji sun kama wata mota dankare da kayan makamai makil a Najeriya

Ba a gama da ASUU ba, ma'aikatan NAFDAC sun tsunduma yajin aiki

A wani labarin, kungiyar ma’aikatan lafiya ta Najeriya (MHWUN) na hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta shiga yajin aikin, The Cable ta ruwaito.

Da yake magana a ranar Laraba a hedikwatar hukumar ta NAFDAC da ke Abuja, shugaban kungiyar Auwalu Yusuf Kiyawa, ya ce yajin aikin ya fara ne daga lokacin da yake magana.

Kiyawa ya ce kungiyar ba za ta janye yajin aikin ba har sai an biya alawus din ma’aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel