Hajj 2022: Mutum biyu daga cikin maniyyata aikin Hajji sun rasu kafin tashin Jirginsu

Hajj 2022: Mutum biyu daga cikin maniyyata aikin Hajji sun rasu kafin tashin Jirginsu

  • Allah ya yi wa wasu Alhazai biyu daga cikin maniyyatan bana daga jihar Kaduna rasuwa tun kafin kwashe su zuwa Saudiyya
  • Maniyyatan biyu sun rasu ne ranar Lahadi da kuma Litinin kuma suna cikin tawagar farko da jirgi zai ɗiba daga Kaduna
  • Gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa Alhazan bankwana kuma ta roki su zama jakadu nagari yayin zamansu a ƙasa mai tsarki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Mahajjata biyu daga yankin ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna, Yakubu Abdulsamad da Haruna Suleiman sun rasa rayuwarsu kafin zuwan ranar tashinsu.

Daily Trust ta ruwaito cewa mhajjatan sun rasu ne ranar Lahadi da Litinin, kafin zuwan ranar tashin su zuwa ƙasa mai tsarki.

Jami'in dake kula da Mahajjatan ƙaramar hukumar, Aminu Surajo, wanda ya sanar da rasuwar su, ya ce tuni aka musu Jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Kara karanta wannan

Hajjin Bana: Maniyyatan da aka yi Garkuwa dasu a Sokoto Sun Samu 'Yanci

Tambarin hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON.
Hajj 2022: Mutum biyu daga cikin maniyyata aikin Hajji sun rasu kafin tashin Jirginsu Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta gano cewa mamatan biyu na na cikin tawagar jirgin farko da zasu tashi zuwa ƙasar Saudiyya daga jihar Kaduna amma Allah ya yi na shi ikon.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana tsammanin kusan mahajjata 2,491 ake sa ran zasu samu damar sauke Farali a Hajjin bana na shekarar 2022.

Gwamnatin Kaduna ta ja hankalin mahajjata

Muƙaddashin gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe, ta kirayi mahajjatan farko daga jihar su zama jakadu nagari yayin zaman su a ƙasa mai tsarki.

Balarabe, yayin da take jawabin bankwana ga mahajjatan a sansanin Alhazai da ke Mando ranar Talata ta bukace su da su saka Kaduna da ƙasar nan a Addu'o'in su.

a jawabinta ta ce:

"Ina godiya ga Allah bisa damar da ya bamu na ganin ranar da kashin farko na Alhazan Kaduna zasu tashi zuwa ƙasa mai tsarki. Na zo muku bankwana ne kuma ina fatan Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya."

Kara karanta wannan

Hajjin bana: ‘Yan bindiga sun tare Maniyyata a hanyar filin jirgi, su na shirin zuwa Saudi

"Sakon mu gare ku shine muna son ku zama jakadu nagari ba ga Kaduna kaɗai ba har da Najeriya baki ɗaya, muna rokon ku samu wani lokaci ku sa kasar mu a Addu'a, ku sa Kaduna a Addu'a kuma ku yi wa shugabannin mu addu'a."

A wani labarin kuma Bayan Tinubu ya lashe zaben, Shugaba Buhari ya faɗi ɗan takarar da yake goyon bayan ya gaje a 2023

Shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ko a baya ya so ayyana Tinubu a matsayin magajinsa na APC.

Ya ce a yanzun bayan ya lashe zaɓen fidda gwani, zai ba shi cikakken goyon baya har ya samu nasara a babban zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel