Yanzu-Yanzu: Bayan shan kaye a zaben fidda gwani, Osinbajo ya taya Tinubu murna

Yanzu-Yanzu: Bayan shan kaye a zaben fidda gwani, Osinbajo ya taya Tinubu murna

  • Mataimakin shugaban kasa ya taya Bola Ahmed Tinubu murnar lashe zaben takarar shugaban kasa a APC
  • Hakan na fitowa ne daga bakin shugaban kungiyar yakin neman zabensa jim kadan bayan fara tattara sakamakon zabe
  • Shugaban ya kuma bayyana irin halin da ya shiga da kuma dadin da yake ji na yiwa Osinbajo hidima a yanzu

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya taya jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu murnar nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Richard Akinnola, mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Osinbajo ne ya taya Bola Tinubu murna, wanda ya lashe zaben kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Business Day ta ruwaito.

Osinbajo ya taya Tinubu murnar lashe zaben fidda gwanin APC
Yanzu-Yanzu: Bayan shan kaye a zaben fidda gwani, Osinbajo ya taya Tinubu murna | businessday.ng
Asali: UGC

Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Yemi Osinbajo, a shafinsa na Facebook, ya ce:

"Ina tayaka murna, Asiwaju Tinubu, wanda ake kyautata zaton ya lashe zaben fidda gwani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A kowace gasa, dole ne a sami wanda ya yi nasara. Duk da haka, ina matukar alfahari da zabi na goyon baya ga Farfesa Yemi Osinbajo."

Ya ci gaba da cewa

“Ba ni da wani nadama game da goyon bayan da nake yi masa. Gata ce taka masa muhimmiyar rawa yayin aikin. Zan sake yin hakan cikin farin ciki a koda yaushe. Magana ce ta yanke hukunci."

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun karade kasar nan, inda suke bayyana Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka kammala.

Haka kawai a saci abu na: Mawaki ya caccaki APC bisa kunna wakarsa a zaben fidda gwani

A wani labarin, tauraron mawaki, Timi Dakolo, ya bayyana bacin ransa tare da nuna rashin jin dadinsa ga jam’iyyar APC mai mulki da ta yi amfani da wakarsa ta Great Nation a lokacin babban taronsu na zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa.

Segalink ne ya jawo hankalin Timi kan yadda APC ta yi amfani da wakar, inda ya tambaye shi ko an biya shi kudin wakarsa?

Segalink ya yada yadda aka kunna wakar kuma ya tambaya cewa: "Dan uwana Timi Dakolo ina fatan za a biya mu a wannan waka da ake yi a babban taron jam'iyyar APC? Great Nation."

Asali: Legit.ng

Online view pixel