Haka kawai a saci abu na: Mawaki ya caccaki APC bisa kunna wakarsa a zaben fidda gwani

Haka kawai a saci abu na: Mawaki ya caccaki APC bisa kunna wakarsa a zaben fidda gwani

  • Shahararren mawakin Najeriya, Timi Dakolo, bai ji dadin jam'iyyar APC mai mulki ba, kuma ya fito fili ya nuna rashin jin dadinsa
  • Mawakin ya mayar da martani ne a lokacin da hankalinsa ya kai kan yadda aka yi amfani da wakarsa mai suna Great Nation a babban taron jam’iyyar na kasa
  • Timi ya yi mamakin dalilin da ya sa za a kunna wakar a irin wannan taron ba tare da izininsa ba, 'yan Najeriya sun masa martani

Najeriya - Tauraron mawaki, Timi Dakolo, ya bayyana bacin ransa tare da nuna rashin jin dadinsa ga jam’iyyar APC mai mulki da ta yi amfani da wakarsa ta Great Nation a lokacin babban taronsu na zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Najeriya ta Dawo Hayyacinta, Za mu batar da Makasan Jama'a, Tinubu Ya Sha Alwashi

Segalink ne ya jawo hankalin Timi kan yadda APC ta yi amfani da wakar, inda ya tambaye shi ko an biya shi kudin wakarsa?

Haka kawai a saci abu na: Mawaki ya caccaki APC bisa kunna wakarsa a zaben fidda gwanin shugaban kasa
Haka kawai a saci abu na: Mawaki ya caccaki APC bisa kunna wakarsa a zaben fidda gwani | Hoto: @timidakolo @apcspecialconvention
Asali: Instagram

Segalink ya yada yadda aka kunna wakar kuma ya tambaya cewa:

"Dan uwana Timi Dakolo ina fatan za a biya mu wannan waka da ake yi a babban taron jam'iyyar APC? Great Nation."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Timi da bai ji dadi ba ya amsa masa da cewa an kunna wakar ba tare da izininsa ba:

"Me zai sa a yi amfani da wakar mawaki ba tare da izininsa ba wajen gangami ko yakin neman zabe. Abubuwan da jama'a ke samu kenan a kasar da ake kira Najeriya. A gaskiya wannan shi ne karo na biyu."

Gani ya kori ji, kalli bayanin da bidiyon:

'Yan Najeriya sun mayar da martani ga Timi Dakolo

Kara karanta wannan

Nwajiuba ya bayyana dalilinsa na rashin zuwa Eagle Sqaure duk da yana takara

Masu amfani da shafukan sada zumunta a fadin kasar sun mayar da martani daban-daban game da yadda Timi Dakolo ya fusata kan amfani da wakarsa ba tare da izininsa ba.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a, ga su a kasa:

_Lolashub:

"Ban gane ba. Idan suka kunna a wajen bikin aure, zai ce haka ne?"

Honee_wealth:

"Babu wani keta hakkin mallaka a nan mana."

Lineofficial:

"Shin majami'u suna biya ne sa'ad da suke rera wadannan wakokin na bishara? Ka dauka cewa ruhu mai tsarki ne ya sa suka yi hakan.”

Uche_vv:

"Sun kunna buga ma, kizz Daniel dole ne ya kai su kara."

Sandypreneur:

"Shin da a ce an gayyace shi a taron zai ce haka?, ganin cewa yana yin haka a mafi yawan tarukan siyasa."

Zaben fidda gwanin APC: Taro ya yi dumi, Osinbajo ya fice daga Eagle Square

Kun ji cewa, Da sanyin safiyar Laraba ne Farfesa Yemi Osinbajo ya bar dandalin Eagles Square inda ake gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na APC, yayin da lamura ke kara fitowa fili cewa burinsa na ya gaji ubangidansa a matsayin shugaban kasar Najeriya mai yiwuwa ya ci tura.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya kauracewa shugaban APC na kasa

Ana kyautata zaton Osinbajo ne kusa da tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a cikin ‘yan takara 23 da ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023, PM News ta ruwaito.

Sai dai abubuwan da suka faru a dandalin na Eagles Square sun nuna cewa mai yiwuwa ba zai samu damar nasara kan mutumin da ya fara nuna masa siyasa ba ta hanyar nada shi a matsayin babban lauya kuma kwamishinan shari’a a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel