Muhimman Dalilai 4 da suka sa Osinbajo ya Sha Mugun Kaye a Zaben Fidda Gwani

Muhimman Dalilai 4 da suka sa Osinbajo ya Sha Mugun Kaye a Zaben Fidda Gwani

Sakamakon wasu dalilai masu yawa, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya sha mugun kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da aka yi inda ya samu kuri'u 235.

Osinbajo ya yi warwas inda tsohon ubangidansa kuma jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya samu kuri'u 1,271 kuma ya tabbata 'dan takara shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa a APC.

Muhimman Dalilai 4 da suka sa Osinbajo ya Sha Mugun Kaye a Zaben Fidda Gwani
Muhimman Dalilai 4 da suka sa Osinbajo ya Sha Mugun Kaye a Zaben Fidda Gwani. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kafin zaben, masu kiyasi sun yi ittifakin cewa ta yuwu Osinbajo ya sha wuya tunda a bayyane ya kalubalanci tsohon ubangidansa, jigon siyasar Najeriya kuma 'dan takarar da yayi caraf da tikitin APC.

Duk da akwai 'yan takara 23 a tseren samun tikitin, 13 daga cikin kwamitin tantancewa ya shawarce su da su janye.

Bayan tattaro dukkan karfin guiwarsa a zaben fidda gwanin, an yi shi cike da adalci kuma, akwai wasu muhimman dalillai da suka tabbatar da rashin nasarar Osinbajo. ga su a jere:

Kara karanta wannan

Najeriya ta Dawo Hayyacinta, Za mu batar da Makasan Jama'a, Tinubu Ya Sha Alwashi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kin goyon bayansa a bayyane da Buhari ya yi

A yayin da ya ke a bayyane cewa Osinbajo na neman kujerar ne tare da amfani da sunan ubangidansa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, babu alamar goyon baya ko kadan daga shugaban kasan kan burin mataimakinsa.

Lalacewar shirin tsayar da 'dan takarar yarjejeniya

Bayan shirun da Buhari yayi, batun tsayar da 'dan takarar yarjejeniya ya taso wanda da an yi hakan zai karfafa burin mataimakin shugaban kasan.

Duk kokarin da shugabancin jam'iyyar ta yi wurin tsayar da 'dan takarar yarjejeniya, ya tashi a kawai.

A yayin da masu lura ke ta hasashen cewa Osinbajo ne zabin Buhari, saboda biyayyar da ya ke masa, Abdullahi Adamu, shugaban APC ya sanar da cewa Ahmed Lawan ne zabin Buhari wanda hakan yasa Osinbajo ya fara cire rai.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 6 da suka marawa Yemi Osinbajo baya akan Bola Tinubu

Rikon da Tnubu ya yi wa yankin Kudu maso yamma

Baya ga kungiyoyin goyon bayan Osinbajo a yankin, Osinbajo a gaskiya ba shi da wani karfin siyasa a yankin wanda zai sa ya ce zai kara da Tinubu kuma ya sha da kyau.

Yadda aka yi zaben fidda gwani da kuma yadda 'yan siyasa kamar su Kayode Fayemi, Ibikunle Amosun suka janye tare da mika wuya ga Tinubu, ya nuna yadda ya ke da kwarjini a yankin ba kamar yadda ake cewa Osun da Legas ce kadai ta shi ba.

Tsarin jam'iyya

Osinbajo ba shi da irin karfin ikon juya 'yan siyasa kamar yadda Tinubu ya ke da shi a shekarun nan.

Tun daga 1993, Tinubu ya tsara jam'iyyun siyasa a matakin karamar hukuma, jiha da kasa.

Wasu daga cikin karfinsa na siyasa sun bayyana ba a Najeriya kadai ba, shi ya taka rawar gani a zaben su tsohon shugaban kasa Jacob Zuma na South Afrika da Shugaban kasa Nana Akufo-Addo na Ghana.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Martanin dan takarar Osinbajo bayan shan kaye a zaben fidda gwanin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel