Dambazau Ya Bayyana Yadda Za a Shawo Kan Matsalar Garkuwa da Mutane Tsakanin Matasan Makiyaya Fulani

Dambazau Ya Bayyana Yadda Za a Shawo Kan Matsalar Garkuwa da Mutane Tsakanin Matasan Makiyaya Fulani

  • Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya) ya yi kira ga cewa a yi gagawan raba matasan Fulani da kwayoyi da makamai
  • Dambazau wanda tsohon minista ne na harkokin cikin gida kuma babban hafsan sojojin kasa ya yi wannan kiran ne a wani taro a Abuja
  • Tsohon ministan ya jaddada bukatar da ke akwai na daukan matakai domin magance garkuwa da mutane tsakanin matasa fulani a Najeriya

FCT, Abuja - Tsohon ministan harkokin cikin gida, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya) ya bukaci a gaggauta karbe makamai da kwayoyi a hannun matasan Fulani a matsayin wani mataki na dakile garkuwa da mutane a kasar.

Dambazau ya yi wannan kiran ne a kasidar da ya gabatar mai taken "Matsalar Makiyaya Fulani" da ya gabatar a taron tsaro na makiyaya fulani a Abuja.

Dambazau Ya Bukaci a Raba Matasan Fulani Da Bindigu Da Kwayoyi
Dambazau ya bada shawarar yadda za a shawo matsalar garkuwa da mutane a tsakanin makiyaya fulani. Hoto: @HonDambazauMHR
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an yi taron ne da nufin gano hanyoyi warware kallubalen da makiyaya fulani ke fuskanta a zamanin nan da nufin samar da tsaro a kasar.

An shirya taron ne da hadin gwiwa da kungiyar Miyetti Allah da Northern Consensus Movement, NCM.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa, daya daga cikin matakan da za a dauka shine dakile samun makamai da kwace dukkan makaman da a yanzu ke hannun matasan fulani makiyaya.

Kalamansa:

"Ya kamata mu tsaftace kasar, ina nufin da taimakon NDLEA, ya kamata a yi yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasan fulani.
"Ya kamata mu tabbatar da adalci da cigaban al'umma da ilimi da lafiyan makiyaya fulani tare da basu damar cigaba a cikin al'umma.
"Don cimma hakan, ya kamata a basu ingantaccen ilimi, lafiya da kuma koyar da su sana'o'i."

Ya ce wata matsala kuma shine wasu makiyayan da ke zama a daji suna satar mutane don karbar kudin fansa.

Ya kara da cewa:

"A baya ana iya gane makiyayi da sandarsa da ya ke kiwon shanu, a yau da AK-47 da wasu makaman ake ganinsu kuma suna amfani da shi wurin kai wa mutanen kauyuka hari ko garkuwa da fasinjoji a manyan hanyoyi.
"An san makiyayi fulani da saukin kai, tausayi, gaskiya, da sadaukarwa amma a yau ana masa kallon dan fashin daji, makashi, mai fyade, barawon shanu da mai garkuwa."

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

A wani rahoton, 'Yan sanda a Abuja a safiyar ranar Laraba 1 ga watan Yunin 2022, sun ceto mutane hudu daga mabuyar masu garkuwa a Dutsen Dudu a unguwar Kuje sun kuma lalata maboyar yan ta'addan.

Rundunar yan sandan ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel