An kuma: Mummunan fashewa ta auku a Kano an rasa shaguna, mutum 20 sun jikkata

An kuma: Mummunan fashewa ta auku a Kano an rasa shaguna, mutum 20 sun jikkata

  • An sake samun mummunan yanayi a jihar Kano, inda tukunyar gas ta fashe ta raunata mutane da dama a wani yanki
  • Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, akalla mutane 20 ne suka jikkata kuma a yanzu haka an garzaya dasu asibiti
  • Hakazalika, an tattaro cewa, shaguna uku sun kone kamar dai yadda hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatarwa manema labarai

Karshen Kwalta, jihar Kano - Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, fashewar iskar gas a wani kantin sayar da man fetur da gas ta kona shaguna tare da raunata mutane 20 a Kano.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru ya rahoto cewa lamarin ya faru ne a wani yanki mai cunkoso a unguwar Sheka, Karshen-Kwalta a Kano.

Kara karanta wannan

Uwa da 'yayanta sun kashe maigida mai rowa saboda cin gadonsa

Tukunyar gas ta fashe a Kano, mutum 20 sun jikkata, shaguna sun kone
An kuma: An sake samun mummunan fashewa a Kano an rasa duniyoyi, mutum 20 sun jikkata | Hoto: blackboxnigeria.com
Asali: UGC

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na daren ranar Alhamis lokacin da wata tukunyar gas ta fashe kuma nan take ta kama wuta.

Gobarar ta lalata wurin da kuma wasu shaguna kusan uku da ke kusa, ciki har da wani bangare na wani gida da ke daura da kantin, inji Vanguard.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda lamarin ya faru

Shaidu sun shaida wa NAN cewa sun ji karar fashewar wata tukunyar iskar gas a daren.

Wani ganau mai suna Malam Abubakar ya ce an garzaya da mutane da dama zuwa asibiti tsirara, yayin da fatun jikinsu suka kone.

Ya ce sama da mutane 10 ne lamarin ya rutsa da su, akasari kuma wadanda ke cikin shagon ne da kuma mutanen da ke kusa da wurin da suke sana’arsu.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Ahmed Idris: EFCC Ta Sako Dakataccen Akanta Janar Da Ake Zargi Da Wawure N170bn

Ya ce mutane 20 ne suka jikkata a lamarin, amma an ceto su da ransu, kuma yanzu haka suna samun kulawa a asibitoci.

Yusif ya ce lamarin ya faru ne sakamakon tsillar wuta daga wani mutum mai soyawa da sayar da kifin da ke kusa da shagon gas din.

Fashewar tulun iskar gas: Hukuma ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a iftila'in Kano

A wani labarin kuwa, adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar tulun iskar gas da ta afku a jihar Kano a ranar Talata ya karu zuwa tara.

Ma’aikatar Agajin Gaggawa ta Tarayya ce ta bayyana haka a lokacin da take sanar da isowar babban daraktan Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa, Mustapha Habib Ahmed, a inda lamarin ya faru, rahoton Punch.

Tun da farko dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane hudu, inda ta ce tulun iskar gas ne ya fashe ba bam ba.

Kara karanta wannan

Gabanin zaben fidda gwani: Kotu ta ba da belin Okorocha a zargin almundahanar N2.9bn da ke kansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel