'An Kashe Kwamandan Boko Haram Da Mataimakinsa' Yayin Da Mafarauta Suka Yi Artabu Da 'Yan Ta'adda a Borno

'An Kashe Kwamandan Boko Haram Da Mataimakinsa' Yayin Da Mafarauta Suka Yi Artabu Da 'Yan Ta'adda a Borno

  • Jaruman mafarauta da yan vigilante sun yi nasarar halaka wani kwamandan Boko Haram da mataimakinsa a Borno
  • Mohammed Yohanna, shugaban kungiyan mafarauta da yan vigilante na yankin arewa maso gabas ne ya tabbatarwa manema labarai hakan a ranar Talata
  • Yohanna ya kuma kara da cewa yayin artabun da suka yi da yan ta'addan sun yi nasarar kwato AK-47 guda daya da babur

Borno - Mohammed Yohanna, shugaban kungiyan mafarauta da yan vigilante na yankin arewa maso gabas ya ce mambobin tawagarsa sun kashe wani kwamandan Boko Haram da mataimakinsa a Borno, rahoton The Cable.

'An Kashe Kwamandan Boko Haram Da Mataimakinsa' Yayin Da Mafarautar Suka Yi Artabu Da 'Yan Ta'adda a Borno
Mafarauta Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Da Mataimakinsa a Borno. Hoto: @thecableng.
Asali: UGC

Yohanna, wanda ya bayyana hakan a hira da aka yi da shi a ranar Talata da manema labarai, ya ce an yi artabu tsakanin yan ta'adda da mafarauta a kauyen Shaffa Taku da ke karamar hukumar Damboa a Borno a ranar Litinin, Vanguard ta rahoto.

Mafarautan sun kwatto AK-47 da babur guda daya

Ya kara da cewa an kwato babur da kuma bindiga AK-47 daga hannun yan ta'addan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun samu bayyanai na sirri daga wurin wasu da suka fada mana yan ta'addan na adamar garuruwansu makonni biyu da suka gabata," in ji shi.
"Bayan samun bayanan, na tattara tawaga ta kuma muka dira wurin da yamma a Shaffa Taku, wani gari da mutane suka tsere daga cikinsu a Damboa.
"Mun yi sa'a, muka hangi yan ta'addan kimanin su 20, kan babura. Muka yi musayar wuta da su kuma muka kashe kwamandansu da mataimakinsa, yayin da saura suka tsere da rauni.
"Mun kuma kwato babur daya da AK-47 guda daga hannun yan ta'addan. Na sanar da jami'an tsaro na bataliya 231 a Biu, kuma za mu hadu a yau domin mika musu AK-47 din da babur."

Yohanna ya kuma ce a halin yanzu mafarautan sun kama wasu mtane da ae zargin suna kai wa yan ta'addan kayan abinci.

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin da kudi Naira miliyan 6.05 a wani kauye a karamar hukumar Hawul.

Ya ce an mika mutanen da aka kama ga jami'an tsaro domin daukan mataki na gaba.

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel