'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

  • Yan sanda da mafarauta a Birnin Tarayya Abuja sun yi nasarar ceto wasu mutane hudu daga maboyar yan bindiga a ranar Laraba
  • Jami'an tsaron sun kai samamen ne a Dutsen Dudu inda suka yi musayar wuta suka kuma fatattaki miyagun sannan suka lalata maboyar
  • Mafarauci guda ya riga mu gidan gaskiya yayin samamen kuma rundunar yan sanda ta mika ta'aziyya ga iyalansa ta kuma yi alkawari cigaba da sauke nauyin da doka ta dora mata

Abuja - Yan sanda a Abuja a safiyar ranar Laraba 1 ga watan Yunin 2022, sun ceto mutane hudu daga mabuyar masu garkuwa a Dutsen Dudu a unguwar Kuje sun kuma lalata maboyar yan ta'addan.

Rundunar yan sandan ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace mutane da yawa, sun kona motoci a wani kazamin hari da suka kai babbar hanyar Kaduna

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane
Yan sanda sun ceto mutane hudu daga maboyar yan ta'adda a Abuja. Hoto: @daily_trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar da ke tabbatar da samamen ta ce:

"Bayan samun bayannan sirri kan wasu yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu mutane a Abuja, yan sanda tare da mafarauta sun tafi Dutsen Dadu ta karamar hukumar Kuje, suka ragargaji yan bindigan, suka lalata maboyarsu sannan suka ceto mutum hudu.
"Samamen da aka kai misalin karfe 6 na safiyar ranar Laraba 1 ga watan Yunin 2022 ya yi sanadin ceto Mustahudeen Sani, Felix Vaa da Adamu wadanda aka sace tsakanin ranar 23 zuwa 25 na watan Mayun 2022 a Kiyi da Abdulsalam Uzugiz da aka sace a Angwan Gade na karamar hukumar Kuje.
"Yayin da yan bindigan suka hangi jami'an tsaron sun yi musayar wuta da su inda wani mafarauci daya ya riga mu gidan gaskiya.
"Bata garin sun tsere da raunin bindiga saboda jami'an tsaron sun fi karfinsu. An kuma kai wadanda aka ceto asibiti don a duba su kafin a sada su da iyalansu."

Kara karanta wannan

'An Kashe Kwamandan Boko Haram Da Mataimakinsa' Yayin Da Mafarautar Suka Yi Artabu Da 'Yan Ta'adda a Borno

Rundunar yan sanda ta bada lambobi da al'umma za su iya kira su yi korafi kan duk wani mutum/mutane da ba su gamsu da shi/su ba

Kwamishinan yan sandan Abuja ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu sannan ya basu tabbacin rundunar za ta cigaba da yaki da laifuka a birnin tarayyar, rahoton The Punch.

Ya bukaci su rika sa ido kuma su sanar da hukuma duk wani abu da ba su gamsu da shi ba.

Ya bada lambobin waya da za iya tuntubarsu cikin gaggawa kamar haka 08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883.

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Kara karanta wannan

Yadda aka tsinci gawarwakin wani dan kasuwa, matarsa da yaransu 3 baje a gidansu

Kamar yadda takardar tazo:

“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel