Ahmed Idris: EFCC Ta Sako Dakataccen Akanta Janar Da Ake Zargi Da Wawure N170bn

Ahmed Idris: EFCC Ta Sako Dakataccen Akanta Janar Da Ake Zargi Da Wawure N170bn

  • Hukumar EFCC ta sako Ahmed Idris, dakataccen Akanta Janar na Najeriya daga wurin da ta ke tsare da shi a ofishinta
  • EFCC ta kama Idris ne a ranar 16 ga watan Mayu kan zarginsa da hannu cikin almunadahar kudade da adadinsu ya tasanma Naira Biliyan 170.
  • Wani daga cikin yan uwan Idris, ya tabbatar da sakinsa yana mai cewa ya koma gida a daren ranar Laraba 1 ga watan Yunin 2022

Hukumar Yaki da Rashawa da Masu Yi Wa Arzikin Kasa Ta'annati, EFCC, ta sako dakataccen Akanta Janar na kasa, Ahmed Idris da ta kama kwanakin baya, Daily Nigerian ta rahoto.

Wasu majiyoyi daga iyalan Ahmad sun tabbatarwa Daily Nigerian da sakinsa inda suka ce a daren ranar Laraba aka sako shi.

Kara karanta wannan

Gabanin zaben fidda gwani: Kotu ta ba da belin Okorocha a zargin almundahanar N2.9bn da ke kansa

EFCC Ta Sako Dakataccen Akanta Janar, Ahmed Idris, Da Ake Zargi Da Wawure N80bn
EFCC Ta Sako Dakataccen Akanta Janar, Ahmed Idris, Da Ake Zargi Da Wawure Biliyoyin Naira. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Facebook

Jami'an hukumar EFCC, a ranar 16 ga watan Mayu ne suka kama Mr Idris kan zarginsa da hannu wurin karkatar da kudade da adadinsu ya kai Naira Biliyan 80.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga bisani an kuma sake alakanta Idris da wata almundahar ta N90bn inda ake zargin ya hada kai da wasu manyan jami'an gwamnati ciki har da wani minista da ba a bayyana sunansa ba.

Mai magana da yawun EFCC, yayin tabbatar da kama Idris ya ce ana zargin an karkatar da kudaden ne ta saka hannun jari a dillancin gidaje a Kano da Abuja.

"Hukumar ta samu ingantattun bayanan sirri da ke nuna AGF ya wawure kudade ta hanyar biyan kwararru na bogi da wasu haramtattun hanyoyi ta hanyar amfani da wasu mutanen da yan uwansa da iyalensa," in ji Mr Uwujaren.

Kara karanta wannan

Zamfara: EFCC ta fadi dalilan da suka ja ta kama tsohon gwamnan Arewa

An nada Mr Idris ne a matsayin Akanta Janar na tarayya a ranar 25 ga watan Yunin 2015 bayan Jonah Otunla ya bar ofishin a ranar 12 ga watan Yunin 2015.

Duk da suka da aka yi ta yi saboda wuce shekarun ritaya, an sake nada shi karo na biyu na shekaru hudu watan Yunin 2019.

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel