Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

  • Mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar da ‘Yan Sanda, PSC, Naja’atu Mohammed ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo
  • Hakan ya biyo bayan yadda ya yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye da Jolly Nyame na Jihar Filato da Taraba
  • Kamar yadda Mrs Mohammed ta ce yayin da RFI ta tattauna da ita, ya kamata Buhari ya gane cewa dukiyar Najeriya ba tashi ba ce

Tsohuwar 'Yar A mutum Buhari, Naja’atu Mohammed, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Afrilu ya yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame
Ba Bu Gwamnatin Da Ta Fi Ta Buhari Rashawa: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu Fitattun Malamai Biyu a Jihar Arewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

A wata tattaunawa da Radio France International, RFI a ranar Litinin, wacce Daily Nigerian ta saurara, Mrs Mohammed ta ce ya dace Buhari ya gane cewa dukiyar Najeriya ba ta shi bace.

A jiharsu ya dace a yafe musu in ji Mrs Mohammed

A cewarta, ya kamata gwamnonin jihohinsu su yafe musu ne, saboda acan suka aikata rashawar, don kundin tsarin mulki ya bayar da yafiya ne ga jihohin da aka aikata laifuka.

Ta kara da cewa yafe wa tsofaffin gwamnonin yana nuna cewa ba a shirya kawo karshen rashawar Najeriya ba. Ta ce kotu ta tabbatar da zargin da ake musu don haka yafiyar na nuna cewa ba a yaki da rashawa a kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Babban Matsala Ga Atiku A Matsayin Dino Melaye Ya Yi Suɓutan Baki, Ya Ce Yan Najeriya Su 'Zaɓi APC', Fani-Kayode Ya Yi Martani

A cewarta:

“Gwamnati ta yi kuskure. Ya dace shugaban kasa ya gane cewa dukiyar al’umma ba ta shi bace. Gwamnatin tarayya ba ta da damar yafe wa wadanda suka tafka laifi a jihohinsu.
“Abu na biyu shi ne wannan yafiyar ta Buhari tana nuna cewa gwamnati ta gaza. Wannan shiyasa muke fama da rashin tsaro. Satar biloniyoyin Filato wacce kotu ta tabbatar, ba za ta rasa alaka da kashe-kashe, tabarbarewar ilimin jihar, lalacewar titina da kashe-kashen da jihar take fama da shi ba.
“Bayan EFCC da kotu sun gama iyakar kokarinsu tsawon shekaru, bai dace kawai ka yafe wa masu laifin ba. Ba kudinka suka sata ba. Me yasa gwamnatin Buhari ta ke yin yadda ta ga dama?”

Ta ce a Tarihin Najeriya ba a taba mulki mai rashawa da sata kamar na mulkin Buhari ba

A cewarta kundin tsarin mulki bai bayar da damar yin wannan haukar ba. Idan haka ne ya kamata a yafe wa ‘yan ta’adda. Saboda babu ta’addancin da ya zarce satar da gwamnonin suka yi.

Kara karanta wannan

Wai Kana Da Gida A Landan Ne? Sarkin Ingila Ya tambayi Shugaba Buhari Jiya

Ta ci gaba da cewa an zabi Buhari ne don ya yi yaki da rashawa, amma yanzu shi ne ya ke yafe wa masu rashawar. Alamu na nuna cewa Buhari ba abin amincewa bane, in ji ta.

Ta ce a tarihi ba a taba gwamnatin da ta fi ta Buhari rashawa ba a kasar nan. Satar da ake yi ta zarce tunani.

A Yayin Da Ortom Ya Yabi Buhari, Wike Ya Masa Kaca-Kaca Kan Yi Wa Dariye Da Nyame Afuwa

A bangare guda, Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya caccaki Gwamnatin Tarayya akan yafe wa tsohon Gwamnan Jihar Filato da na Jihar Taraba, Joshua Dariye da Jolly Nyame, wadanda aka daure akan rashawa, rahoton The Punch.

Wike, wanda dan takarar shugaban kasa ne na PDP, ya ce afuwar alama ce da ke nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta raina wa ‘yan Najeriya hankali kuma siyasa kawai take yi ba yaki da rashawa ba.

Kara karanta wannan

Sauye-Sauyen NNPC: "Rayuwa Ta Na Cikin Hatsari", Kyari Ya Yi Magana Kan Barazanar Kashe Shi

Wike ya yi wannan maganar ne yayin da ya kai ziyara wani yanki na Jihar Neja don kamfen ga wakilan jam’iyyar PDP sakamakon yadda zaben fidda gwani yake kara matsowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel